Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Dogarawan Tsaro Na Juyin Yuya Hali a Iran


Jiya Asabar ne wasu ‘yan bindiga sun bude wuta a wajen wani faretin sojoji a Kudu maso yammacin Iran, inda suka kashe akalla mutum 25 da raunata wasu 60, a cewar kafar yada labarai ta gwamnati.

Jami’ai sunce an kashe ‘yan bindigar biyu. Wasu kuma rahotanni na cewa an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a kai harin.

Kungiyar IS da wata kungiyar larabawa ta gwagwarmayar ‘yan to Ahvaz, sun dauki alhakin harin da aka kai yankin Khuzestan.

Kafar labaran Iran, ta ce maharan sun kai harin ne wani waje da jami’an kasar suka taru domin kallon faratin da aka saba yi duk shekara, domin murnar zagayowar ranar da aka kafa jamhuriyar musulunci a tsakanin alif 980 zuwa alif 988 bayan yaki da kasar Iraqi. An gudanar da makamancin wannan fareti a wasu sassan kasar.

Akasarin mutanen da suka mutu dogawan tsaro na juyin juya halin kasar Iran ne. haka kuma wasu rahotanni na cewa daga cikin wadanda suka mutu din akwai wani dan jarida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG