Shugaban Amurka Donald Trump, jiya Lahadi, yayi ikirari ba tare da ya gabatar da wata shaida ba cewa, binciken da ake gudanarwa kan danganatakr kwamitin yaken neman zabensa a 2016 da kasar Rasha, doka bata amince dashi binciken ba.
A wani mataki da ba a saba gani ba, Fira Ministan Pakistan Imran Khan a jiya Lahadi ya bada sanarwar cewa gwamnatinsa zata bada shaidar zama dan kasar ga dubun dubatan 'yan gudun hijira daga Afghanistan wadanda kasar ta basu muhalli na shekaru masu yawan gaske.
A farkon makon daya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu ‘yan mata bakwai, daga garin Girnashe na karmar hukumar Isa a jihar Sokoto.
Ethiopia da Eritrea, sun sanya hanu kan wata yarjejeniya a wani taron koli da suka yi a kasar Saudiyya, matakin da ya kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, wadanda suka kwashe shekaru 25 suna yaki da juna.
Shugaba Buhari ya daga hannun sakataren jam’iyyar APC Mai Mala Buni, biyo bayan zabar sa da gwamna Ibrahim Gaidam ya yi don takarar gwamnan jihar Yobe, a jam’iyyar APC a zaben 2019.
Kungiyoyin agaji 19 sun yi kira cikin gaggawa a dauki matakan kawo sauki ga bakin haure sama dubu 17, dake cunkushe a wata cibiya dake tsibirin Girka, wajen da aka gina da zummar tsugunnar da mutane dubu 6. A cewar wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar tun ranar Alhamis.
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya yiwa shugaban ‘yan adawar kasar dake daure afuwa, Victoire Ingabire Umuhoza.
Tsananin guguwar nan mai lakabin Florence ya ragu zuwa mataki mummunar guguwar da aka saba gani, bayan da ta afkawa jihar North Carolina, dauke da iska mai karfin gaske da kuma ruwa kamar da bakin kwarya, inda ta yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane biyar.
Gwamnatin jihar Yobe ta amince da wasu dokoki masu tsanani, ciki har da daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin fyade ga kananan yara.
Kungiyar IS ta dauki alhakin harin kunar bakin waken da aka kai ranar Litinin a shelkwatar kamfanin mai na kasar Libya dake birnin Tripoli, bisa ga cewar kungiyar ayyukan leken asiri ta Amurka da ake kira SITE, wadda ke sa ido kan masu tsatsautsauran ra’ayi.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, fadar White House a shirye take tsaf, yayin da guguwar teku take kadowa ta dira a gabar tekun gabashin kasar.
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga bangarorin Syria su guji tsunduma yaki gadan gadan.
Kungiyar Fulani makiyaya ta Najeriya MIYETTI ALLAH da kungiyar sarakunan gargajiya ta Kirista sun cimma wasu kudurorin zaman lafiya don kawar da baragurbi da kan kawo fitina a tsakanin al’umma.
Bayan fiye da shekaru 30 da gwamnatin jihar Kano ta mallaka gonakan wasu al’umomin kimanin kauyuka bakwai ga jami’ar Bayero, yanzu haka wasu daga cikin al’umomin na ikirarin diyyar gonakai daga mahukuntan Jami’ar.
Bakin haure sama da 100 sun mutu bayan da kwalekwalen balam-balam da ke dauke da su guda biyu su ka samu matsala a cikin tekun Bahar Rum bayan sun baro gabar Libiya a farkon wannan wata na Satumba.
Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un ya aika da wasikar bukatar sake ganawa a karo na biyu da Shugaban Amurka Donald Trump, a cewar fadar Shugaban Amurka ta White House a jiya Litini.
Amurka, jiya Litini, ta ce ba za ta ba da hadin kai ba ta kowace fuska ga Kotun Kasa da Kasa ta Shari'ar Manyan Laifuka dake birnin Hague, muddun ta gudanar da bincike kan zargin aikata laifukan yaki da ake ma sojojin Amurka da kuma jami'an leken asirinta a kasar Afrghanistan.
Sakamakon ambaliyar da ruwa da aka samu sama da kadada dubu 75 na gonakin shinkafa ne suka lalace a jihar Neja, dake arewacin Najeriya.
Yanzu haka dai ana cece-ku-ce a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, reshen jihar Adamawa, bayan da kanin matar shugaban ‘kasa Dakta Mahmood Halilu Ahmad ya fito takarar kujerar gwamnan jihar.
Ciki da Gaskiya Wuka Ba Ta Hudashi
Domin Kari