Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rik Machar Ya Yi Watsi Da Gayyatar Shugaba Salva Kiir


Shugaban 'yan tawaye a Sudan ta kudu Rik Machar, yayi watsi da gayyatar da shugaban kasar Salva Kiir yayi masa a jiya Asabar, ya kai ziyara Juba babban birnin kasar.

Machar wanda shine shugaban kungiyar 'yan tawaye da ake kira SPLMIO a takaice, ya gayawa KIiir a wani taro a birnin khartoum cewa, yanayi a Juba bai dace da ziyara daga tawagar 'yan tawaye ba.

Yace Ina tsaro, Ina da damuwa kan haka. Hakika, idan zamu aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya akwai bukatar haka ga mutane da zasu dawo juba daga yankunan 'yan tawaye. Hak nan Machar yace a tattaunawa da suka d a shugaba Kiir ta woyar tarho, yace yayi kira ga shugaban ya sake fursisnoni ciki harda na siyasa.Yace hakan zai bada karfin guiwa da karfafa yarda tsakanin sassan kasar.

Shugaba Kiir, wand a yake jagotantar jam'iyyar SPLM, yace bangarensa ya saki dukkan fursinoni zuwa watan Disemba.

A halin da ake ciki kuma kamfanin dillancin labarai na Reuters yace hukumar kula da tasaro cikin ruwa ta Najeriya da ake kira NIMASA a takaice tace ma'aikatan jirgin ruwan MV Glarus da 'yan fashin teku suka kama a Najeriya, bakwai daga cikin su 'yan kasar Phillipines ne, saura sun fito ne daga kasashen Slovenia,Ukraine, Romania, da Croatina, d a Bosnia.

Jami'an Najeriya suka ce har yanzu ba'a san inda 12 daga cikin ma'aikatan jirgin suke ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG