Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Binciken Da FBI Ke Yiwa Brett Kavanaugh


Fadar Shugaban Amurka ta White House, jiya Lahadi, ta ce sam ba ta jujjuya binciken da hukumar FBI take yi ma mutumin da aka gabatar da sunansa don zama Alkalin Kotun Kolin Amurka, Brett Kavanaugh.

"Lauyan fadar White House ya bar Majalisar Dattawa ta fayyace iyaka da kuma hurumin binciken," abin da Jami'ar Yada Labaran Fadar White House Sarah Huckabee Sanders ta gaya ma tashar telebijin ta Fox News kenan jiya Lahadi, game da binciken da hukumar FBI ke yi kan zargin yinkurin fade da wata macce mai suna Dr. Christine Blassey Ford ta yi ma Kavanaugh.

Da Kavanaugh da Ford duk sun ba da ba'asi a lokuta dabam-dabam a gaban Kwamitin Shari'a na Majalisar Dattawa ranar Alhamis da ta gabata. Ford ta gaya ma Kwamiti din cewa ta yi imani 100 bisa 100 cewa Kavanaugh ya nemi yin lalata da ita karfi da yaji a 1982, lokacin dukkansu biyu matasa ne 'yan makarantar sakandare, a yayin da shi kuma wanda ke fuskantar tantancewar zama Alkalin Kotun Kolin ya karyata zargin a fusace.

Shugaban Amurka Donald Trump, ranar Jumma'a, ya ba da umurnin a yi sabon bincike kan Kavanaugh kamar yadda kwamitin ya bukaci a yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG