Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici Ya Sake Barkewa a Wasu Unguwanni Na Kwaryar Jos


Hukumomin tsaro a jihar Filato sun bukaci al’umma dake ciki da wajen jihar da su gargadi matasa dake neman tayar da zaune tsaye a jihar su rungumi zaman lafiya.

Kiraye-kirayen ya biyo bayan wata hatsaniya ne a wasu unguwannin cikin kwaryar Jos, wanda ya kai ga rasa rayuka da kona gidaje da ya zuwa yanzu ba a tantance ba.

A cewar kwamandan rundunar tsaro ta STF, Manjo Janar Augustine Agundu, lamarin ya kasance da takaici ganin irin zaman tattaunawar da su ka yi da matasan karamar hukumar Jos ta arewa, kwatsam sai wani rikicin ya sake barkewa.

Shima kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Undie Adie, wanda ya bayar da sanarwa ta kafafen yada labarai ya bukaci mutane su kasance a cikin gidajensu. Ya ci gaba da cewa “duk wanda aka kama a waje za a damke shi a kuma hukunta shi.”

Da yake yiwa Muryar Amurka karin haske kan lamarin, Kwamishinan yada labarai, Yakubu Datti, ya ce lamarin ya baiwa kowa mamaki ganin yadda aka zauna da shugabannin addinai da shugabannin matasa da na unguwanni, inda kowa ya mika kai cewa za a yi tafiya tare sai gashi wannan rikici ya sake barkewa.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG