Ciki da Gaskiya Wuka Ba Ta Hudashi
Cikin dare daya an kara samun wani Biloniya a jihar South Carolina, bayan da aka sayar da tikitin cacar lottery a jihar da kudinta ya kai dala Biliyan 1 da miliyan 537.
Matar gwamnan jihar Kebbi, Hajiya Zainab Bagudu, ta baiyana cewa gidauniyar da ta ke jagoranta mai suna “MEDICAID” za ta gudanar da sabon gangami a bana ta hanyar tattaki a tsakiyar Abuja don fadakar da jama’a illar cutar daji da kan hallaka majinyaci in ba a samu matakin wuri ba.
Mai baiwa shugaban Amurka shawarar kan harkokin tsaron ‘kasa John Bolton, ya nuna alamun yarjejeniyar makamai da Amurka ta cimma da Rasha bata da wani sauran amfani.
Kungiyar tsaron NATO tace an kashe daya daga cikin sojojinta tare da raunata wasu guda biyu a harin da aka kai lardin Herat na Afghanistan.
An ayyana dadadden shugaban kasar Kamaru Paul Biya amatsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar ranar 7 ga watan Oktoba. Sai dai jam’iyyun adawa sun nuna rashin amincewa da sakamakon zaben, amma Majalisar tsarin mulki ta yi watsi da korafe-korafen a soke zaben.
Da alama matasa zasu sauya alkiblar mulki da siyasar kasar Afghanistan, kasancewa matasa da dama sun tsaya takarar neman madafun iko a matakai dabam dabam na kasar.
Amurka ta dauki mataki a hukumance a jiya Laraba na ficewa daga wata dadaddiyar kungiyar kasa da kasa, a wani yunkurin rage tsadar farashin aikawa da kananan kaya kasashen waje a Amurka.
An fara gudanar da binciken musabbabin mutuwar a kalla mutane bakwai a cikin wata zanga zangar bayan zaben kasar Zimbabwe.
Masu ruwa da tsaki a jami’iyyar APC a jihar Nasarawa sunyi wani zama na musamman da ‘yan takarkaru da suka fafata a zaben fidda gwani don dinke duk wata baraka da ka iya kunno kai a jami’iyyar.
Wani dalibi mai shekaru 18 ya harbe ya kashe mutane 19 kana ya jikata sama da wasu hamsin a wata kwalejin kere kere a Crimea.
Gwamna jihar Neja a Najeriya Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce ya zama tilas shugabannin siyasa su dauki matakin shawo kan kisan jama’a da yaki ci yaki cinyewa a jihar Filato dake Arewacin kasar.
A wani yunkuri na kawo fahimtar juna a tsakanin al’ummomin yankin Mambilla dake jihar Taraba, inda akayi ta samun tashe-tashen hankula, cibiyar kawo fahimtar juna a tsakanin Musulmi da Kirista ta kasa da kasa sun ziyarci yankin tare da shirya gangamin fadakarwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 17 ga watan Oktoba domin bukin tunawa da ranar yaki da talauci, wace ta samo asali a 1992 bayan da aka gano cewa talauci na kokarin samun gindin zama a kasashe masu tasowa.
Duk da yake Najeriya na daya daga cikin kasashen da ake lissafawa da habakar tattalin arziki, to amma kuma kasar ta na cikin jerin kasashe mafi tsananin talauci a duniya.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kulle kokofin shiga Majalisar Dokoki, biyo bayan wata wasikar da kakakin Majalisar ya aikawa ‘yan Majalisar cewa an dage zaman Majalisar saboda da wani aiki daya taso a Abuja.
Kungiyar Amnesty International da gwamnatin Amurka, sun nuna damuwa bisa yadda ‘yan Boko Haram suka kashe ma'aikaciyar agajin nan Hauwa Liman dake aiki da kungiyar Red Cross.
Domin Kari