Wani rahoton kungiyar bincike da kididdiga akan matakin talauci a duniya, ya nuna cewa Najeriya a yanzu, ta kasance babbar cibiyar fatara da matsanancin talauci a duniya, mukamin da ta ture kasar Indiya ta dare a kai.
Rahoton ya bayyana cewa kimanin adadin ‘yan Najeriya miliyan 87, da ke wakiltar kusan kashi 50 cikin 100 na yawan jama’ar kasar, suna rayuwa ne a cikin matsanancin talauci, musamman ma a yankunan karkara.
A baya-bayan nan ma, kididdiga ta nuna cewa jihohin Arewacin Najeriya, su ne suka fi yawan matalauta a duk duniya, da adadinsu ya kai kashi 85 cikin 100 na jama’ar yankin.
Wannan yanayi dai na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatoci a Najeriya suke da’awar fitowa da tsare-tsare masu manufar yaki da fatara da samar da ayukan yi, wadanda manazarcin lamurran siyasa da tattalin arziki, Dr. Mansur Isah Buhari, yake ganin basu yi wani tasiri ba.
Wannan sabon matsayi na talauci a Najeriya, ya saka shakku da tababar samun nasarar muradun wanzar da ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya, na kai karshen matsanacin talauci ya zuwa shekara ta 2030, a dai dai lokacin da kuma ake fargabar lamarin zai fi Kamari ya zuwa shekara ta 2050, sa’adda ake hasashen samun karauwar yawan jama’a a kasar.
Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk Sanyinna.
Facebook Forum