Mafi yawan wadanda suka fito takara a zaben ‘yan Majalisun Afghanistan da za a yi ranar Asabar matasa ne. Yawancinsu ‘yan shekaru 20 zuwa 30.
Mai karancin shekaru cikin ‘yan takarar zaben ‘yan Majalisu shine mai shekaru 26 da haihuwa, shekara daya tal ya dora a shekarun da mutum zai iya tsayawa takara wanda yake 25. A cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta Afghanistan, sama da kashi 50 cikin 100 na ‘yan takarar da zasu fafata a zaben na ranar Asabar matasa ne.
Mafi yawan ‘yan kasar Afghanistan suna ‘yan ‘kasa da shekaru 25 a cewar asusun kididdiga na Majalisar Dinkin Duniya, kuma ‘yan siyasar matasan na yunkurin ganin sun karbe ikon kasarsu nan gaba.
Wata matashiya 'yar takara da Muryar Amurka ta yi hira da ita, Maryam Samaa tace rabin al'ummar kasar matasa ne sabili da haka ya kamata a dama da su a harkokin siyasa da mulkin kasar
Tace “Kada mu manta, sama da kashi 60 cikin 100 na yawan al’ummarmu matasa ne. Kamata yayi su kawo canji, kuma kamata yayi ace suna cikin wadanda ke kafa dokoki da kuma gudanar da su.”
Magoya bayansu na fatan cewa ‘yan takarar zasu yi watsi da son kai, da na iyali domin ciyar da kasa gaba. Yawancin ‘yan takarar kuma suna da ilimi sama da sauran matasan kasar, kuma suna da sanin yadda harkoki ke tafiya a sauran kasashen duniya.
Facebook Forum