Daraktan kungiyar Amnesty a Najeriya Osai Ojighbo, ya ce wannan kisan rashin imanin da aka yiwa Hauwa mohammed Liman, wacce ke taimakawa mutanen da tarzomar Boko Haram ta rutsa dasu a shiyyar arewa maso gabas, kuma suke matukar bukatar taimako, wannan kisa laifin yaki ne, kuma dole a kare ma'aikatan agaji.
Amnesty International ta ce dole ne Boko Haram su sako daya ma'aikaciyar agajin da ta rage a hanunsu, sannan dole mahukuntan Najeriya su kara kaimi wajen kubutar da daruruwan fararen hula da ke hanun Boko Haram, ciki har da Leah Sheribu dalibar makarantar Dapchi daya tilo da ta rage a hanunsu.
Daga karshe Amnesty International ta ce lalle duk wadanda suka taka rawa wajen laifukan yaki da ma cin zarafin bil'adama a Najeriya dolene a gurfanar dasu gaban shari'a.
A daya bangaren kuma, ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya aike da sakon jaje da ta'aziyya ga iyalan Hauwa Liman bisa wannan aika-aika, inda Amurkan ke cewa zata ci gaba da aiki tare da kawayenta irin su Najeriya don murkushe ta'addanci. wannan kisa dai na ci gaba da jan hankalin ‘yan Najeriya irin su sabo imamu Gashua dake kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta bude kofar tattaunawa don ceto sauran wadanda Boko Haram ke garkuwa da su.
In za a iya tunawa, a watan maris ne Boko Haram suka kai hari a garin Rann da ke jihar Borno, inda sukai awon gaba da ma'aikatan agajin guda uku, wato Saifura Hussein Ahmed khorsa, Hauwa Mohammed Liman da Alice Loksha, a watan jiya mayakan suka kashe saifura kana a wannan mako kuma suka kara kashe Hauwa.
Yanzu dai abin jira a gani shine irin matakan da gwamnatin shugaba Buhari za ta dauka wajen kubutar da ma'aikaciyar jin kai daya tilo dake hanunsu.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum