Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojan Kungiyar NATO a Harin Afghanistan


Dakarun kungiyar NATO a Afghanistan
Dakarun kungiyar NATO a Afghanistan

Kungiyar tsaron NATO tace an kashe daya daga cikin sojojinta tare da raunata wasu guda biyu a harin da aka kai lardin Herat na Afghanistan.

Kungiyar Taliban ta yi da’awar mutumin da ya kai harin a matsayin daya daga cikin dakatunta wanda yake ‘daya daga cikin sojojin Afghanistan.

A halin yanzu kuma, rundunar sojojojin Amurka ta tabbatar da cewa birgediya Janar dinta yana daga cikin Amurkawa biyun da suka raunata a harin da aka kai na makon jiya a Afghanistan, wanda ya raunata shguaban ‘yan sandan kasar.

Birgediya Janar Jeffrey Smiley, dake jagorantar rundunar tsaron NATO a Afghanistan, yana daya daga cikin wadanda ‘dan bindigar dake sanye da kayan sojojin Afghanistan ya harba, lokacin da ya budewa jami’an wuta yayin da suke barin wajen ganawar da suka yi da kwamandan NATO a Afghanistan, Janar Scott Miller.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG