Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Take Ranar Yaki Da Talauci a Duniya


Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 17 ga watan Oktoba domin bukin tunawa da ranar yaki da talauci, wace ta samo asali a 1992 bayan da aka gano cewa talauci na kokarin samun gindin zama a kasashe masu tasowa.

Miliyon mutane ne aka kiyasta cewa suna fama da talauci a duniya matsalar da ake dangantawa da rashin kudade a hannun jama’a sakamakon rashin aikin yi, ko kuma sana’oin dogaro da kai dalili kenan da MDD ta ware ranar 17 ga watan Oktoba domin tayar da gwamnatoci daga barci.

Koda yake talauci wani abu ne da a can baya ake dangantawa da harakokin tattalin arziki, MDD na ganin girman wannan matsala ya fice inda ake zato lura da yadda rashin mutunta ‘yancin dan adam ke karawa jama’a radadin wannan al’amari.

Jamhuriyar Nijer na daga cikin kasashen da ake sakawa a jerin kasashe masu fama da talauci duk kuwa da cewa Allah ya azurta ta da albarkatun karkashin kasa, saboda haka masana ke gargadi akan wasu mahimman ababen da aka yi imani suna yanke talauci.

Hukumomin jamhuriyar Nijar wadanda tun da jimawa suka hango bukatar bullo da matakan cike gibin da karancin amfanin gona ke haifarwa a karshen damuna, sun yi tanade tanade da dama don bunkasa aiyukan noman rani wanda ta wani bangare ke matsayin babban makamin yaki da taluci.

Wasu alkaluman da kungiyoyin kasa da kasa suka bayar na nuni da cewa daga cikin mutane 4 dake fama da talauci a Nijer 3 dukka mata galibinsu mazauna karkara.

A karkashin taken ranar yaki da talauci ta bana MDD ta yi kiran jama’ su hada kai da mutanen da aka gwadawa wariya domin girka sabuwar duniyar da za a mutunta ‘yanci da mutuncin dan adam a duk inda yake a duniya, abin da ke fayyace sabbin kamannin da talauci ke bijirowa gwamnatoci da kungiyoyin kare hakkin bil adama.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:21 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG