Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Hadin Kan ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa


Gwamnan Jahar Nasarawa, Alhaji Tanko Al-Makura
Gwamnan Jahar Nasarawa, Alhaji Tanko Al-Makura

Masu ruwa da tsaki a jami’iyyar APC a jihar Nasarawa sunyi wani zama na musamman da ‘yan takarkaru da suka fafata a zaben fidda gwani don dinke duk wata baraka da ka iya kunno kai a jami’iyyar.

Mutane 11 ne suka tsaya neman takarar gwamna a jami’iyyar ta APC a jihar Nasarawa, yayin da mutane bakwai suka tsaya yin takarar Sanata, sai mutane 29 suka yi takarar Majalisar wakilai, mutane 117 kuma suka tsaya takarar ‘yan Majalisar jahar ta Nasarawa.

Sakataren jami’iyyar APC a jihar Nasarawa, Aliyu Bello, ya ce makasudin taron shine su kira wadanda basu sami nasara a zaben fidda gwanin ba don su goya baya wa wadanda suka yi nasara don cimma burin jami’iyyarsu.

Itama Mary Enwongulu wacce ta tsaya takarar Sanata amma bata yi nasara ba, ta ce ta hakura kuma zata goyi bayan wanda yayi nasara.

Shiko Gwamnan jihar ta Nasarawa, Umaru Tanko Almakura ya ce taron yayi tasiri don duk ‘yan takarar da suka fadi zaben sun rungumi kaddara da alkawarin zasu yi wa jami’iyyar aiki ta kai ga nasara a zabe mai zuwa na shekarar badi.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG