Ciki da Gaskiya Wuka Ba Ta Hudashi
Hukumomin kasar Pakistan sun tsare daga baya suka bada belin wata fitattar ‘yar gwaggwarmaya yayinda take komawa kasar, ko da yake sun rike takardar Passpo dinta. Inji ‘yar gwaggwarmayar.
Asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF -ya bada rahoto cewa, galibin yara da suke zaune a yankunan da aka sami bullar cutar Ebola a Damokaradiyar Jamhuriyar Congo sun koma makaranta, inda aka koya masu yadda zasu kare kansu daga kamuwa da cutar.
Kwamitin ayyukan jinkai na kasa da kasa yana rokon gaggawa ga kungiyar mayakan Najeriya dake mubaya’a da kingiyar IS a Afrika ta Yamma, ta saki ma’aikatan lafiya biyu da tayi garkuwa dasu farkon shekarar nan.
An ware kananan yara ‘yan kasa da shekaru 18 daga cikin ‘yan kungiyar sa kai ta Civilean JTF, an kuma mika su ga asusun tallafawa kananan yara na MDD.
An gudanar da gangami don bunkasa shuka ingantaccen iri daga tsakiyar Abuja zuwa ma’aikatar gona da ke anguwar Area 11.
A wani sabon yunkuri na magance matsalar mace-macen mata da kananan yara a Najeriya, gidauniyar matar shugaban ‘kasa Aisha Buhari ta kaddamar da shirin gina wasu dakunan kula da mata da kananan yara a manyan Asibitocin Najeriya, wanda tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.
Kamfanin sada zumunta na Facebook ya sanar da cewa ya goge wasu shafuka sama da 800, wadanda yawancinsu a Amurka suke, kuma suna yada labarun karya da suka shafi siyasa.
‘Yan sandan Tanzania sun toshe kusan dukkan hanyoyin shiga da fice na birnin Dar es Salam, a kokarin da suke na gano wani hamshakin attajiri da aka sace, wanda ke zama matashin da yafi kowanne matashi kudi a nahiyar Afirka.
Hukumar zaben kasar Kamaru ELECAM, ta ce ta samu korafe-korafe har 25 na kiran a soke zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Lahdin da ta gabata.
Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga tsohon mataimakinsa dan takarar shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar.
Majalisar Dattawan Najeriya ta roki gwamnatin tarayya cewa ta kafa kwamitin bincike mai karfi da zai sa a gano Janar Idris Alkali, wanda ya bace tun watan da ya gabata.
Jami’an sojan Najeriya da hadin gwiwar na kasar Chadi sun ce sun hallaka ‘yan kungiyar Boko Haram 124 a wasu hare-hare daban-daban da su ka kai musu.
Da yawan ‘yan kasar Sudan suna kokawa game da yadda gwamnatin Sudan din ta sake rage darajar kudin kasarta ranar Lahadi, da kusan rabi, yayin da tattalin arzikin kasar ke cikin halin kaka-ni-kayi.
Amurka tana tuhumar wani ‘dan leken asirin kasar China da laifin yunkurin satar bayanan sirri na cinikayya daga wasu manyan kamfanonin jiragen sama da na hanyoyin sufurin sama.
Jiya Laraba mahaukaciyar guguwar nan da aka radawa sunan Michael ta afkawa wani yankin jihar Florida, wadda ke zama guguwa mafi karfi a tarihi da ta taba afakawa doron ‘kasa a Amurka cikin shekaru 50.
Jami’an hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya NAPTIP ta mikawa jami’an diplomasiyyar Ghana wasu ‘yan mata takwas da aka so yin safararsu zuwa kasashen Larabawa.
Turkiya ta nemi izinin a jiya Litinin daga Saudi Arabia ta binciki ofishin jakadancin Saudiyar a Istanbul, domin gano dalilin bacewar wani dan jaridar Saudi Arabia da jami’an Turkiya suka ce an kashe shi a cikin ofishin jakadancin.
Kasar Kamaru ta fara kirga kuri’ar da aka kada a zaben shugaban kasa na ranar Lahadi, wanda jamai’ai da masu sa ido na kungiyar Tarayyar Afrika suka kwatanta da mai inganci.
Majalisar Dokokin Najeriya za ta dawo aiki daga hutun ta na shekara da ta tafi, sai dai daga dukan alamu za ta dawo cikin ruguntsumin shugabanci duba da yadda shugabanin ta biyu suka chanja sheka daga jam’iyyar APC mai mulki kuma mafi rinjaye a Majalisar zuwa ta PDP mai adawa.
Domin Kari