Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Trump Ta Amince Da Fara Shirin Mika Mulki Ga Biden


Zababben shugaban Amurka Joe Biden.
Zababben shugaban Amurka Joe Biden.

Hukumar da ke hidima ga cibiyoyin gwamnatin tarayyar Amurka (GSA a takaice), ta tabbatar cewa zababben shugaban kasa Joe Biden, shi ne a ta bakinta, “wanda, ga alama ya yi nasara” a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba.

Shugaba Donald Trump, wanda ya ki amincewa da sakamakon zaben, ya fadi jiya Litini cewa, ya ba da umurni ga jami’an gwamnatinsa, su bayar da hadin kai ga kwamitin karbar mulki, to amma ya sha alwashin cigaba da fafatuka.

Wannan matakin ya share fagen harkokin mika mulki da gwamnatin Trump ka yi, tare da barin Biden ya samu hadin kan cibiyoyin gwamnatin tarayya, game da shirin karbar mulki ranar 20 ga watan Janairu.

A wata wasikar bayyana daukar wannan mataki, da shugabar hukumar ta GSA, Emily Murphy, ta rubuta ma zababben shugaban kasa Joe Biden, ta ce, “Don Allah, a fahimci cewa, don radin kaina na yanke wannan shawarar, bisa ga tanajin doka da kuma tabbatattun bayanai. Sam, babu wani jami’i daga bangaren zartaswa da ya taba matsa mani lamba – ciki har masu aiki a fadar shugaban kasa ta White House ko wannan hukuma ta GSA – kan irin shawarar da na yanke da kuma lokacin da na yanke shawarar.”

Trump ya kafe sakonsa a shafin ta na Twitter jim kadan bayan an bayyana wasikar ga jama'a: "Lamarin mu zai ci gaba, za mu ci gaba da ... yakin, kuma na yi imanin za mu yi nasara! Duk da haka, don amfanin Kasar mu, ina ba Emily da tawagarta shawarar su yi abin da ya kamata a yi kamar yadda tsari ya samar, kuma na fadawa tawaga ta su ma su yi hakan. "

A safiyar jiya Litinin, Senata Lamar Alexander mai ritaya daga Tennessee, wanda ke ta kiraye-kirayen a fara shirin mika mulki, ya fitar da wata sanarwa da ke cewa ya kamata Trump "ya sanya kasa a farko" kuma ya taimaka wa gwamnatin Biden ta yi nasara.

XS
SM
MD
LG