Kananan yara sun koma Makarantu tsakanin karshen watan Satumba da farkon watan Oktoba,lokacin da yawan masu kamuwa da cutar ke ‘kasa da kashi biyu cikin 100.
Har ila yau a ranar Laraba, karamar hukumar Clark ta jihar Nevada, wadda ta hada da birnin Las Vegas, ta kaddamar da wata manhajar waya da ake kira "FixIt," inda mazauna yankunan za su iya ba da rahoto game da batutuwa ciki har da sabawa dokar coronavirus.
A ranar Talata, garin New Orleans ya sanar da cewa zai soke jerin gwanon bikin Mardi Gras a watan Fabrairu, saboda cutar Corona na ci gaba da karuwa a yawancin Amurka.
A can jihar California kuma, birnin Los Angeles ya umarci gidajen cin abinci da gidajen sayar da barasa wadanda ke budaddun wuraren ajiye mutane, da su rage adadin kwastomomin su zuwa kashi 50 cikin 100, kuma su rufe da 10 na dare. Rufaffun wurare kuma, kamar shagunan da ba su da mahimmanci sosai sun rage adadin mutanen da suke samu zuwa kashi 25 cikin 100 kawai, yayin da sauran wuraren kasuwanci kamar dakunan gyaran gashi na iya ba da sabis kawai ga wadanda suka kira suka bada lokacin zuwa.
Ana daukar dukkan wannan matakan ne domin shawo kan sake yaduwar cutar coronavirus.