Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Trump Ya Ce Biden Ya Yi Nasara Amma Da Magudi


Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.
Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.

Jiya Lahadi, a karon farko, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna ya amince da cewa dan takarar Demokrat Joe Biden "ya lashe" zaben shugaban kasa kusan makonni biyu da suka gabata, amma sanadiyyar magudi.

A cikin wasu kalamai da ya yi ta kafewa a shafin Twitter, Trump ya ci gaba da wasu maganganu ba tare da gabatar da hujja ba, cewa an kayar da shi ne da magudi.

Shugaban, dan jam’iyyar Republican, ya ki amincewa da shan kaye a zaben a hukumance ga tsohon Mataimakin Shugaban kasar, duk da cewa duk manyan kungiyoyin yada labarai na Amurka sun ce tsawon mako guda Biden ya tara fiye da adadin da ake bukata na kuri’u 270 a cikin kuri’un wakilan kwaleji 538 don lashe zaben shugaban kasa da za a kaddamar ranar 20 ga watan Janairu.

A cikin wani bayani, Trump ya fadi game da Biden cewa, "Ya yi nasara ne saboda an yi magudi a zaben."

Shugaban ma’aikatan fadar White House mai jiran gado a gwamnatin Biden, Ron Klain ya fada wa shirin Meet the Press na NBC cewa sakon Twitter da Trump ya fitar ba shi ne zai maida Biden shugaban kasa ba, kuma ba shi ne zai hana masa zama Shugaban kasa ba. Amurkawa ne kadai za su tabbatar da haka.

Jami’an zabe a fadin kasar sun fada wa Muryar Amurka da wasu kafafen yada labarai cewa basu gano wata shaidar tafka magudin zabe ba sai dai wasu ‘yan kananan matsaloli na kidaya kuru’u a ranar zabe wadanda ba za su iya sauya nasarar da Biden ya yi ba, kana ba za su iya bai wa Trump damar yin tazarce na wani wa’adin shekaru hudu a fadar White House bA.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG