Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ba Da Umarnin a Sake Kidaya Kuri'un Jihar Georgia a Zaben Amurka


Masu Kidayar Kuri'u a Jihar Georgia.
Masu Kidayar Kuri'u a Jihar Georgia.

Babban jami’in zabe a jihar Georgia da ke kudancin Amurka ya ba da umarnin a sake kidayar kuri’un zabe da hannu wanda aka yi tsakanin Shugaba Donald Trump da zababben Shugaban Joe Biden.

Kusan duk kuri’un da aka kidaya a Georgia, mai kalubalantar Trump na Democrat mai neman wa’adin shekaru hudu a Fadar White House na kan gaba da kuri’u 14,112 daga cikin kuri’u kusan miliyan biyar da aka kada a jihar.

Sakataren jihar Georgia Brad Raffensperger, dan jam’iyyar Republican, ya ce yana son Trump ya ci zaben, amma ya musanta ikirarin da ‘yan Republican ke yi cewa kirgan kuri’un na Georgia akwai kura-kurai. Jihar Georgia ba ta zabi dan takarar shugaban kasa na Democrat ba tun 1992.

Yayin da yake sanar da sa ido a sake kidayar kuri'un na Georgia, Raffensperger kewaye da jami'an zaben yankin kuma ya nuna goyon baya da jinjina ga aikinsu.

Ya ce zai gayyato duka masu sa ido na Democrat da na Republican don kallon sake kirga kuri'un saboda halin da ake ciki.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG