Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Mamakin Ingancin Allurar Rigakafin Coronavirus Da Kamfanin Amurka Ya Samar


Allurar Rigakafin Coronavirus Ta Kamfanin Pfizer
Allurar Rigakafin Coronavirus Ta Kamfanin Pfizer

Gwajin rigakafin cutar coronavirus da kamfanin Pfizer ya samar, ya nuna sakamako mai kyau da ya wuce yadda aka yi tunanin samu a baya.

Kamfanin harhada magungunan nan na Pfizer, ya ce gwajin baya bayan nan na rigakafin COVID-19 da ya kirkiro, ya nuna yana da ingancin sama da kashi 90 cikin 100, wanda hakan ya zarce abin da aka zata a baya, wanda hakan kuma ya zama labari mai kyau kan yakin da ake yi da cutar coronavirus.

Shugaban kamfanin Pfizer, Albert Bourla ne tare da kamfanin da ke taimaka ma Pfizer, BioTech, su ka yi wannan shelar ranar Litinin game da mataki na uku wanda shi ne na wajejen karshe, na binciken da su ke yi kan wannan rigakafin na su.

Bayanin nasu na cewa, binciken da ake yi ya nuna cewa, rigakafin na da ingancin fiye da 90 cikin 100, wajen kare wadanda su ka sha, muddun ba su dauke da cutar tun farko.

Babban kwararre kan cututtuka masu yado a Amurka, Dakta Anthony Fauci, ya fadi a wata hira da manema labarai ranar Litinin cewa, wannan sakamakon, a ta bakinsa, “abin mamaki ne.”

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG