Sabuwar gwamnatin jihar Zamfara ta gwamna Dauda Lawal ta ce sam ba za ta bi sawun tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ba wajen yin sulhu da 'yan bindiga.
Babban Ministan Lafiya na Najeriya Dr. Muhammad Ali Pate ya ce akwai likitoci da sauran jami'an lafiya sama da 400,000 a Najeriya amma ba su wadatar ba don haka akwai bukatar kari.
Rasuwar babban malamin addinin musulunci na Ahlussunnah a Najeriya Sheikh Abubakar Giro Argungu ya girgiza jama’a da dama inda shafukan yanar gizo su ka cike da ta’aziyya.
Yau Laraba Kotun sauraron karar zaben Shugaban kasa za ta yanke hukumci bayan kwanaki dari da rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban kasa.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana kwarin guiwar samun nasara a kotun sauraron karar zabe da za ta yanke hukunci a Larabar nan kan karar kin amincewa da sakamakon da ya kawo Ahmed Bola Tinubu karagar mulki.
Kungiyar Fulani makiyaya ta MIYETTI ALLAH KAUTAL HORE ta ce iilmantar da 'ya'yan makiyaya ne kadai hanyar raba su da miyagun iri.
Masanin kimiyyar siyasa na jami'ar Abuja Dr. Farouk B.B Farouk, ya ce korafin wata jiha ta samu karami ko babban Minista ya sabawa tsarin dimokradiyya.
Tawagar manyan malaman Islama na Najeriya da ta gana da shugaban gwamnatin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ta ayyana nasarar ziyarar.
Domin Kari