In za a tuna kotun karar zabe karkashin Haruna Tsammani ta kori karar jam’iyyar PDP, LP da APM ta bai wa Tinubu na APC nasara.
Tun zaben 2003 da tsohon shugaba Obasanjo da mataimakinsa Atiku suka lashe ba a daina tafiya kotun koli ba har yanzu.
Sai a 2015 ne bayan Jonathan ya fadi zabe ya zabi barin matakin kalubalantar zaben.
Kalaman tsohon shugaba Muhammadu Buhari a zuwan shi kotun koli na karshe a 2011 na nuna ba ja da baya ga garzayawa kotu.
Mai taimakawa shugaba Tinubu kan labaru Abdul'aziz Abdul'aziz ya ce in da ma an samu daya daga alkalan kotun karar zabe ya ga gaskiyar 'yan hamayyar da za su iya tsammanin wani tagomashi a kotun koli.
Tuni dai dan takarar PDP Atiku Abubakar ya umurci lauyoyi su daukaka kara don watsi da sakamakon kotun karar zabe.
Jigon kamfen din PDP Yusuf Dingyadi ya ce suna sa ran hujjojinsu za su gamsar da kotun koli.
A na su bangare, kakakin kamfen na Peter Obi na Leba Malam Yunusa Tanko ya nuna akwai dalilai da za su sake gabatarwa da ke nuna shugaba Tinubu bai ma cancanci takara ba.
Ba a dai yi wa kotu riga-malam, amma a tarihin shari'ar zaben shugaban kasa ba a taba sauke shugaba a kotun koli ko umurni da a sake zabe ba amma an yi a kan gwamnoni da majalisar dokoki.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna