A cewar sabuwar gwamnatin, bin tsarin sulhu da tsohuwar gwamnatin ta yi ya janyo kara tabarbrewar tsaro a jihar.
A taron manema labarai a Abuja, sabuwar gwamnatin ta ce za ta yi garambawul ga dukkan matakan tsaro da tsohuwar gwamnatin ta buge a kan su da ta ce ba su haifar da wani sakamako mai ma'ana ba.
Mannir Mu'azu Haidara shi ne kwamishinan labaru na jihar "sam ba za mu yi sulhu da 'yan ta'adda ba don haka za mu dau 'yan sintiri 300 a kowace karamar hukuma don gamawa da miyagun irin."
A martninsa, kakakin tsohon gwamna Zailani Bappah ya ce ko gobe suka samu dama sai sun dawo da sulhu.
"A duk wata fitina da a ka yi a duniya karshe dole sai an dawo teburin sulhu don samar da maslaha." Ya ce.
Kwamishina Mannir Haidara ya zargi jami'an tsohuwar gwamnatin da yin warwason kayan gwamnati bayan faduwa zabe.
A nan kuma Zailani Bappah ya aza alhakin warwason kan zauna gari banza "An yi dukan mu da kona gidajen mu har sai da 'yan sanda su ka buga bindiga."
Sabuwar gwamnatin ta ce mukamin karamin minista tsaro da a ka ba wa Bello Matawalle bai tsole mata ido ba tana mai cewa tun a kujerar gwamna ma bai tabuka komai ba ta fuskar tsaro.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna