Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAUREN MATASA: Yadda Damina Ta Kankama Amma 'Yan Bindiga Sun Hana Shiga Gonaki Da Ke Nesa Da Gari, Kashi Na 3 - Agusta 21, 2023


Nasiru Adamu
Nasiru Adamu

Shirin har ila yau na garin Dan Umaru ne mai albarkar matasa manoma da ke karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi arewa maso yammacin Najeriya.

Matasa sun taru a zauren inda su ka koka da cewa ga dai damuna ta kankama amma miyagun iri sun hana shiga gonaki da ke nesa da gari. Matasan na bukatar dauki daga hukumomi don kar hakan ya zama barazana ga samar da abinci yayin da janye tallafin fetur ya jefa talakawa cikin kuncin rayuwa.

Ra'ayin matasa na nuna ko dai ba za a samu yin noman yanda a ka saba ba; to mutane su samu yin barci da ido biyu rufe.

A makon jiya Yahuza Gado na magana kan yanda wasu matasan su ka yi hijira daga yankin su ka nufi kudancin Najeriya ko kurmi don neman sabbin sana’o’i.

Saurari shirin:

ZAUREN MATASA
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:10:01 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG