Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu Ta Girgiza Jama’a Da Dama


Sheikh Abubakar Giro Argungu (Hoto: Facebook/Sheikh Abdullahi Bala Lau)
Sheikh Abubakar Giro Argungu (Hoto: Facebook/Sheikh Abdullahi Bala Lau)

Rasuwar babban malamin addinin musulunci na Ahlussunnah a Najeriya Sheikh Abubakar Giro Argungu ya girgiza jama’a da dama inda shafukan yanar gizo su ka cike da ta’aziyya.

Sheikh Argungu wanda shi ne shugaban kwamitin gudanar da ayyuka na kungiyar Izala, ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya a birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana juyayin rasuwar Sheikh Giro Argungu wanda ya bayyana a matsayin mutumin da ba ya kasa a guiwa kan dukkan aiyukan alheri da ya sa a gaba.

Sheikh Bala Lau ya ce za a gudanar da jana'izar marigayin a garin sa Argungu yau alhamis din nan bayan sallar azahar.

Gabanin wannan rasuwa ta Sheikh Argungu an taba samun lokaci sau daya ko sau biyu a baya da a ka yayata rasuwar malamin in da lamarin ya zama ba haka ba ne.

An yi wa marigayin tambaya a lokacin inda ya nuna hakan ya tunatar da shi cewa mutuwa na nan tafe.

Sheikh Giro ya shahara ainun a fagen wa'azin sa na koyarwa a majalisun karatu da kan mumbari a ciki da wajen Najeriya da ma musamman a Makkah da Madina.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG