Tawagar manyan malaman Islama na Najeriya da ta gana da shugaban gwamnatin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ta ayyana nasarar ziyarar.
Fadar shugaban Najeriya ta Aso Rock ta ce ba ta yi zaben tumun dare ba a nada tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC.
Firaministan jamhuriyar Nijar Ouhoumoudou Mahamadou ya sauka a Abuja Najeriya don jiran yanda za ta kaya a matakan da kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma ECOWAS ta dauka na ba da wa’adin maida mulki hannun farar hula daga sojojin da su ka kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum.
Jama'a na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabambanta game da matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da umarnin su maida mulki hannun farar hula.
Jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya ta ce ba wanda ya tilastawa Sanata Abdullahi Adamu yin murabus daga shugabancin jam'iyyar.
A hirarsa da wakilin Muryar Amurka, daraktan yada labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya ce mataimakin shugaban jam'iyyar na arewa Sanata Abu Kyari ke jagorantar jam'iyyar.
Mai ba wa shugaba Tinubu shawarwari kan lamuran siyasa Ibrahim Kabir Masari ya ce wasu ‘yan damfarar siyasa na karbar kudi daga hannun wasu da sunan za su sa shugaba Tinubu ya nada su Ministoci.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa zai yi iyaka iyaka domin ganin an fidda talakawa daga kuncin rayuwa.
An shafe daren jiya a Najeriya ana yayata jerin sunayen wadanda ake cewa, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ke shirin zaba a matsayin Ministoci, a kafofin sada zumunta na yanar gizo duk da yake babu wata majiya a hukumance da ta tabbatar da haka.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta ce cire tallafin fetur ba tare da matakan rage radadi ga talakawa ba zai jefa akasarin jama'a cikin karin kuncin talauci.
Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce za ta cigaba da hukunta duk jam'ian ta da ta samu da laifi a lokacin gudanar da babbar zaben 2023 da ya gabata.
Domin Kari