Kwamitin raya yankin arewa maso gabas na bukatar Naira Tiriliyan biyu cikin shekaru goma, don aikin raya yankin arewa maso gabas da hakan zai baiwa dukkan wadanda suka rasa muhallansu damar komawa garuruwansu na asali.
Kungiyar da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya kafa don kawar da shugaba Buhari daga mulki ta shiga jam’iyyar adawa ta ADC, da nanata kudirin kawo sabbin jini a harkokin siyasa.
Babban bankin Najeriya CBN da na kasar China sun shiga yarjejeniyar musayar kudin kasashen biyu, don saukaka huldar kasuwanci ba tare da neman dalar Amurka ba.
Gwamnatin Najeriya ta hana shigowa ko sarrafa duk wani ruwan maganin hana tari dake ‘dauke da sinadarin Codeine.
Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da karar tuhumar shugaban kungiyar Shi’a na kasa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da laifin kisan kai.
Kalubablen rashin guraban aiki da karancin albashi shi ne ke haddasa likitoci da jami’an jinya na ungozoma da suka yi karatu a Afirka, su fice zuwa kasashen ketare, musamman na turai domin yin aiki.
Yayin da zaben shekarar 2019 ke karatowa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC na cewa ta dauki matakan hana duk wani magudi.
Alkalin babbar kotun tarayyar Najeriya Justice Gabriel Kolawale, ya janye daga wata shari’a da ta shafi tsohon mai bada shawara kan tsaro Kanal Sambo Dasuki.
A kokarin taimakawa alhazan Najeriya su saukar da aikin ibadar wannan shekarar hukumar alhazai ta bukaci Saudiya ta kara cibiyoyin daukar shaidar tambarin yatsun mutum kazalika an kira gwamnati ta ragewa alhazan farashin dala
Sanarwar da kakakin fadar shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar ta ce shugaban yana iyakar kokarinsa wajen cika alkawuran da ya yi lokacin neman zabe saboda yaki da cin hanci da rashawa da inganta tsaro da kuma habaka tattalin arziki ne shugaban ya sa gaba
Najeriya na ci gaba da bunkasa noma da sarrafa shinkafa, matakin da ya sa har wasu kamfanonin Thailand guda bakwai sun durkushe saboda Najeriya ta daina sayen shinkafarsu
Sa’oi kadan bayan da kotun tarayya ta ba da belin Maryam Sanda, matar da ake tuhuma da kashe mijinta, Bilyaminu Bello a Abuja, babban Birnin Najeriya, masana shari’a sun fara fashin baki kan wannan hukunci.
Jigogin wannan kungiya wadanda suka hada da Attahiru Bafarawa da Ibrahim mantu sun ce makasudin wannan gamayya ta su shine maido da tasirin siyasar da suka ce linzaminta ya kubuce ma 'yan arewa
Hukumar INEC ta Najeriya ta karawa ma'aikatanta girma har zuwa matakin aikin gwamnati na goma sha biyar. Sannan kuma a Jihar Zamfara ana takaddamar tantance Kwamishinan zaben da suke kiki-kakar cewa ba dan asalin jihar ba ne shi yasa ba zasu amince da shi ba.
Babban taron PDP ya caza manyan ‘yan jam’iyyar da nuna babu barin baya da ‘kura da zai shafi tasirin jam’iyyar a zaben shekarar 2019.
An zabi Uche Secondus a matsayin sabon shugaban babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, bayan da aka kammala kidaya kuri'un zaben da aka gudanar jiya Asabar.
Akwai alamu da ke nuna cewa, mai yiwuwa akai ruwa rana a babban taron da jam'iyar PDP mai adawa ke yi a Abuja, bayan da gwamnonin kudu maso kudu suka nuna alamun goyon bayan dan takarar da ya fito daga yankinsu a matsayin dan takarar shugaban jam'iyar.
Hadaddiyar kungiyar matasan arewacin Nigeria ta janye umarnin korar yan Kabilar Igbo daga arewacin kasar, amma ta gitta wasu sharudda.
Domin Kari