Shugaban hukumar alhazan Najeriya Barrister Mukhtari Abdullahi Muhammad ya bukaci Saudiya ta kara cibiyoyin daukan tambarin yatsun alhazan Najeriya domin saukakawa alahazai 95,000 saukin samun biza.
Shugaban yana tattaunawa ne akan lamuran harkokin aikin haji a kafar gidan talibijan naMinara mallakar kungiyar IZALA, ya ce yanzu cibiyoyin daukan tambarin uku ne kacal. Inji shugaban gwamnatin Najeriya na tattaunawa da gwamnati Saudiya ta yadda alhazan Najeriya ba zasu sha wahala ba.
Shugaban gidan talibijan din Imam Abdullahi Bala Lau ya ce kungiyar ta kafa gidan talibijan din ne da zummar domin bunkasa addinin Islama da zaman lafiya a tsakanin al'ummar Najeriya. Ya kira gwamnati ta sake duba farashin dala ga aikin hajji.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum