Hukumar zaben Najeriya wato INEC, ta daga likkafar wasu dimbin ma’aikatanta ta hanyar kara musu girma bisa matakan aikin gwamnati daban daban har zuwa matakin aikin da ya kai na 15 wato abinda ake cewa level 15 a Turance don kara zaburar da su, kamar yadda Kakakin hukumar Aliyu Bello ya bayyana.
Wannan karin girman dai ya zo ne gab da kakar zabukan siyasar Najeriya a matakai daban daban. Wanda kuma ana sa ran yin hakan zai karawa ma’aikatan hukumar ta zaben kasar azamar aiwatar da aikinsu kamar yadda ya kamata.
To amma kuma a wani hannun sai ga wata takaddama ta taso daga jihar Zamfara a daidai lokacin nan da ake tantance kwamishinonin zaben da za’a Makala a kujerun shiyyoyi. Abinda ya faru kuwa shine, ba’a tantance wani mutum daya ba daga jihar ta Zamfara don bashi mukamin na kwamishinan zaben jihar.
Hakan ya faru ne biyo bayan wata takarda da aka gabatarwa majalisar tarayyar Najeriya da ke nuna cewa, wanda ake son tantancewar Ahmad Mahmud bad an asain jihar Zamfara ba ne. Wanda hakan tasa Sanata Kabiru Marafa ya maida martanin cewa dole ayi adalci ga Mahmud.
Ya kara da cewa, Gwamnan jihar Abdul’aziz Yari da ake zargin ya tura takardar ne ma za a ce bad an Zamfara ba. Domin kuwa bayanai sun nuna cewa an haifi Mahmud ne a garin Gusau, kuma yayi kwamishina har shekaru hudu a jihar Zamfaran.
Kakakin jam’yyar APC reshen jihar Zamfara Sani Gwamna, yayi watsi da batun Sanata Marafa da cewa Ahmad ba dan jihar Zamfara bane, kuma ko da dan jihar ne ba zasu amince da wakilcinsa ba domin kuwa Mahmud din bai bautawa jam’iyyarsu ta APC ba.
Ga cikakken rahoton wakilinmu daga Abuja, Najeriya.
Facebook Forum