Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben APC Ya Bar Baya Da Kura


Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci
Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci

Dan Majalisar Dattawa daga jihar Kaduna,Sanata Suleiman Hunkuyi yace sun mika korafi ga hedikwatar Jam'iyyar APC mai mulki cewa ta soke zaben unguwanni na jam'iyyar a Kaduna don zargin nadi aka yi ba zabe ba.

Hunkuyi ya kara tabbatar da rade-radin manyan 'yan APC a jihohi dabam-dabam da ba su gamsu da yadda zaben ya gudana ba, cewa, za su fice daga jam'iyyar.

"Mun ja layi, mun gayawa magabata na APC cewa idan suna bukatar a yi APC tare da jama'a, to wajibi a yi gyara." inji Hunkuyi

A bangaren wadanda suka gamsu da zaben shine Inuwa Yahaya da ya bayyana cewa an yi nasarar kara hada kan APC domin 2019.

"An turo mana mutane da suka san yanayin zabe kuma suna 'yan zabe kuma daman 'yan siyasa ne gogaggu."

Saurari cikakken rohoton Nasiru El Hikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG