Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Da Obasanjo Ya Kafa Ta Koma Jam’iyyar ADC


Olusegun Obasanjo
Olusegun Obasanjo

Kungiyar da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya kafa don kawar da shugaba Buhari daga mulki ta shiga jam’iyyar adawa ta ADC, da nanata kudirin kawo sabbin jini a harkokin siyasa.

Dagewar da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi kan sukar gwamnatin Buhari, ya fara fusata mukarraban da nuna bani na iya ke damunsa.

Tsohon shugaban dai ya ce gwamnatin Buhari ta gaza don haka take bugewa da cewa ta samu kalubale ne daga tsohuwar gwamnatin PDP. Ya kara da cewa idan babu kalubale me ya sa Buhari ya hau mulki ne, kuma yake son yin tazarce?

Ya’u Chiroman Bakan Daura, dake zama mukarrabin Buhari ya ce kawaicin shugaba Buhari yayi yawa domin inda Obasanjo ya tabo wasu daga cikin tsaffin sojoji da ya sami amasar da ta dace da shi.

Shi kuma Abubakar Sa’idu Nafada, dake rajin kawo sabbin jini a jam’iyyar APC, ya ce amma hakan ba zai hana dagewa wajen sake zabar shugaba Buhari a 2019 ba.

Haka kuma matasa sun bayar da gudunmawarsu wajen zaben Buhari, kuma matasan Najeriya sun shirya don karbar mulki bayan Buhari ya kammala wa’adin shekaru takwas dinsa.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG