A wani mataki na ganin an magance matsalolin da masu manyan motoci suke haifarwa, kama daga bata hanyoyi zuwa haifar da hadurra a duk fadin Najeriya, hukumomin kasar na shirin samar da wuraren dakatarwar motocin a sassan kasar.
An Fara jigilar maniyyata hajjin Najeriya zuwa kasar Saudiya domin gudanar da aikin hajjin bana. An bude aikin jigilar ne da alhazan Abuja, babban birnin kasar.
Ana kara samun bayanai kan halin da shugaban Najeriya ke ciki tun bayan da ya tafi jinya a birnin London a watan Mayu, a baya-bayan nan wasu gwamnonin kasar ne suka kai mai ziyara inda suka ce sun sami shugaban cikin yanayi mai kyau.
Yayinda yake jawabi a mijami'ar fadar shugaban kasa dake cikin Aso Villa mukaddashin shugaban Najeriya Farfasa Yemi Osin bajo ya bukaci duk shugabannin mijamiun Najeriya da su yi waje da duk masu halin bera dake tsakaninsu.
Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya na kara ba da tabbacin cewa hukumar da aka amince a kafa ta raya arewa maso gabashin Najeriya da rikicin Boko Haram daidaita za ta fara aiki.
Kwararru a taron kwamitin shugaban Najeriya mai tallafawa Arewa maso Gabas, sun gano cewa gina gidaje nesa da juna a yankunan Borno na samawa ‘yan ta’adda saukin afkawa jama’a.
Shugaban jam’iyyar PDP Sanata Ali Modu Sheriff ya shiga ofis a hedikwatar jam’iyyar ta Wadata Plaza dake Abuja.
Wata kotun tarayyar Najeriya ta yankewa wata mata hukuncin ‘dauri bayan da aka same ta da laifin yunkurin safarar hodar iblis daga Najeriya zuwa Saudiya.
Kungiyar matasa Kristoci masu wanzar da salama da kuma reshen matasa na kungiyar Kristocin Najeriya CAN sun gudanar da taron wanzar da zaman lafiya a birnin Abuja.
Gwamnatin Najeriya ta amince da turawa jihohi kudi fiye da Naira Biliyan 522, don tallafawa jihohin su biya bashin da ma’aikata suke binsu na albashi da fansho.
Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotanni dake cewa an samu bullar cutar Polio ko kuma a shan-inna a kudu maso kudancin kasar, bayan da aka haifi wani yaro da nakasa a jikinsa.
Umarnin da shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya bawa ministan Shari’a Abubakar Malami, na cewa ya gudanar da bincike kan kowaye aka samu da laifin zarmiya a gwamnatinsa da alwashin gurfanar da duk wanda aka samu da laifi gaban kotu.
Kungiyoyin manoma dake raya kiwo da noma a yankunan karkara sun gudanar da wani taro a birnin Abuja, gabannin babban taron Ministocin aikin gona na kungiyar ECOWAS.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar bakwai ga watan Disamba don tunawa da kuma bunkasa harkar sufurin jiragen sama na fararen hula.
Babban kotun tarayyar Najeriya ta bayar da hukuncin a saki Mallam Ibrahim El-Zakzaky cikin kwanaki 45, a kuma bashi diyyar Naira Miliyan 50.
Ministan ya rasa ransa ne tare da dansa lokacin da motarsu tayi hadari kan hanyar Abuja zuwa kaduna.
Yayin da akasarin talakawa ba su maida hankali ga abubuwan dake haddasa sauyin yanayi, kwararru su na gargadin cewa idan ba a yi wani abu yanzu da sauri ba, illar da zata yi zai rutsa da dukkan bil Adama.
A zaben bana, jam'iyyun siyasa a Najeriya sun rungumi sabon salon bakanta juna maimakon mayarda hankali kan abubuwan da suka yi ko zasu yi ma jama'a.