Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana iyakar kokarinsa wajen cika alkawuran da ya dauka lokacin da yake neman kujerar shugaban kasa.
A sanarwar da Garba Shehu, kakakin fadar shugaban kasa ya fitar, shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta dage kan tsaro, inganta tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa domin dawo da Najeriya kan turba.
A cewar shugaban, yankunan da 'yan Boko Haram suka fi addaba zasu ba da shaida idan suka kwatanta yadda suke rayuwa can baya da yanzu.
Shi ma sakataren APC, Mai Mala Buni ya ce su suka san yadda kasar take musamman lokacin da suke nema zabe. Yankin arewa maso gabas tamkar ya zama mallakar Boko Haram ne a lokacin. Ya ce kasar ta kusa durkushewa saboda babu tsaro, babu zaman lafiya.
Inji Mai Mala dawowar Shugaba Buhari kan mulki abubuwa suka fara daidaituwa, al'amuran rayuwa suka soma tabbata.
Su ma jami'an tsaro cewa suka yi an ga bayan 'yan ta'adda dalili ke nan yanzu suke farma fararen hula da basu da kariya sosai.
Malaman Islama irinsu Abdullahi Bala Lau na ganin gwamnatin Buhari na iya kokari saidai a tayata da addu'a nmusamman domin samun nasarar ceto 'yan matan Dapchi kamar yadda aka samu nasara akan ceto wasu 'yan matan Chibok.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum