Tsohon mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP Prince Uche Secondus ne ya lashe zaben shugabancin jam'iyyar bayan kammala babban taron jam'iyyar da ya kawo karshen kwamitin riko na Sanata Ahmed Makarfi.
Secondus daga yankin kudu maso kudancin Najeriya, ya samu kuri’u 2000 inda ya yi nasara kan abokan takarar sa biyu Farfesa Tunde Adeniran da Chief Raymond Dokpesi.
Tun gabanin taron, wassu daga wadanda su ka aiyana tsayawa takarar da su ka hada da Bode George da Gbenga Daniel sun janye; inda har George ke zargin cewa gwamnan Rivers Nyesom Wike ya nunawa Yarbawa wariya musamman don mara baya ga Secondus.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar daTom Ikimi da sauran gwamnonin jam'iyyar irin su Ayo Fayose da Ibrahim Dankwambo sun shaida sanarda sakamakon da a ka yi daidai karfe uku da minti goma sha biyar na safe agogon Najeriya.
Yanzu jam'iyyar za ta tura tikitin takarar shugaban kasa yankin arewa a shekarar 2019.
Alamu na nuna har yanzu gwamnoni na da tasirin juya lamurra a manyan jam'iyyun Najeriya.
Facebook Forum