Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Fulani Ta Nuna Damuwa Kan Yadda Ake Far wa Fulani A Najeriya


Taron Kungiyar Fulani ta Jonde Jam.jpg
Taron Kungiyar Fulani ta Jonde Jam.jpg

Yayin da wasu al'ummomi a Najeriya ke ci gaba da fuskantar hare-haren da suke tuhumar Fulani barayi ke kai wa, ita kuwa kungiyar Fulani ta kasa ta kara kokawa akan cin zarafi da ta ce ake yi wa Fulani a kasar.

SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da kungiyar ke mayar da martani akan kisan wani Bafillace da aka yi a Sokoto da sunan jagoran barayin da suka addabi jama'a, wanda kungiyar ta ce ba wanda ake tuhuma ne ba aka kashe.

Ayukkan ‘yan bindiga na ci gaba da tunzura ‘yan Najeriya abin da kai wasu lokuta har jama'a na daukar doka da hannunsu.

Irin haka ne ya faru a Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, makon da ya gabata inda jama'ar garin Gigane tare da masu aikin tsaro na sa kai suka yi wa wani Bafilatane kisan gilla da sunan cewa shi ne Charande jagoran barayin da ke addabar yankunan Illela, Gwadabawa da wasu sassan da ke gabashin Sakkwato.

Sakataren kungiyar Fulani na kasa Bello Aliyu Gotomo ya ce yadda ake cin zarafin Fulani ya yi yawa, domin ko kwanannan an tare wani bafulatane a garin Kware ta Sokoto aka kama shi aka kashe aka yi gunduwa-gunduwa da namansa.

Ya ce da ace wanda ake tuhuma ne wato Charande aka kashe da su kansu sun ji dadi an kashe ‘dan ta'adda, amma wannan da aka kashe Sarkin Fulani Shehu Asara ne, kuma da yana da illa da ba'a ba shi sarautar Sarkin Fulani ba.

Wani mazaunin garin ya ce jama'ar garin sun kashe mutumin ne lokacin da ‘yan sa kai suka kamo shi suka sheda musu cewa shi ne Charande, kuma a cewar shi, yanzu haka barayi sun fara kai wa garin na Gigane hare-hare.

Har ila yau daya daga cikin shugabannin al’ummar garin, wanda baya so a ambaci sunan sa, yace tabbas Charande ne aka kashe duk da yake daga baya suna jin kananan maganganu cewa ba shi ne ba.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bakin mukaddashin kakinta a Sakkwato ASP Ahmad Rufa'i ya bayyana cewa basu da tabbacin wanda aka yi wa kisan gillar saboda basu san Charande a fuska ba kuma ba wanda ya zo a hukumance ya shedawa rundunar cewa ba shi ne aka kashe ba.

Acewar kakakin suna da masaniyar kisan kuma sun yi kokarin hana faruwarsa amma abin ya gagara, amma dai yanzu haka suna kan bincike akan lamarin.

Kungiyar ta Miyetti Allah ta ce yanzu Fulani suna fuskantar barazana a wasu wurare na Najeriya domin ba da jimawa ba an halaka wasu Fulani makiyaya 10 a yankin Mashegu na jihar Neja.

Masana na ganin cewa wannan lamarin dai idan ba'a kula ba yakan iya haifar da mummunan matsala fiye da yadda ake gani yanzu, akan hakan ne kungiyar ta ce zata tunkari mahukunta don neman daukar matakan da suka dace domin takaita lamarin.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Kungiyar Fulani Ta Nuna Damuwa Kan Yadda Ake Far wa Fulani A Najeriya.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG