Duk da yake har yanzu ana samun yaduwar miyagun kwayoyi cikin al'umma a Najeriya, hukumar da ke yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi tana ci gaba da kokarin ganin an samu raguwar yaduwar su.
Daraktar kula da harkokin shara'a da gabatar da wadanda ake tuhuma da laifi a gaban shara'a ta hukumar NDLEA Joshpene Ruth Obi wadda ta maganta da yawun shugaban hukumar Muhammad Buba Marwa, ta ce a cikin watanni 29 hukumar ta kama masu tu’ammali da kayan maye da yawansu ya kai dubu 32.
Daga cikinsu akwai gagagan diloli 35. Ta kwace kayan maye masu nauyin kilo gram miliyan 6 da dubu 300, kuma ta lalata wurin da ake noman tabar wiwi mai fadin kadada 852, da dai sauran nasarori da ta samu.
A matakin jihohin Najeriya ma jami'an hukumar a Sakkwato da ke arewa maso yammacin kasar, sun kona kayan maye masu nauyin kilogram fiye da dubu 25 da kiyasin kudin su ya kai daruruwan miliyoyin naira.
Kumandan hukumar a Sakkwato Muhammad Iro Adamu ya ce shi ya nuna cewa kayan maye da suke kwacewa ba komai suke yi da su ba, kamar yadda wasu jama'a ke tababa, suna nema izni ne a wurin kotu kafin su kona kayan.
Masu ruwa tsaki a fafatukar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi na fargabar cewa, kayan da hukumar ke kamawa adadin su kan iya zama kadan daga cikin wadanda ke zagayawa a cikin al'umma da ba'a sami nasarar kamawa ba, kamar yadda Nura Attajiri ke cewa.
Hukumar ta yaki da sha da safarar kwayoyi ta ce hakan ne ya nuna akwai bukatar shigowar jama'a ga fafatukar.
Shugabannin al'umma ma suna da gagarumar gudunmuwar da ya kamata su bayar domin ceto jama'ar su daga fadawa cikin wannan matsala. Akan haka ne gwamnatin jihar Sakkwato ta ce shirye take ta yi aiki da hukumar NDLEA domin ceto jama'ar ta daga fadawa cikin wannan ta'asar.
Masu fafatuka dai a wannan haujin na fatar ganin gwamnati da sauran jama'a sun yi da gaske domin a sami nasarar kawar da mummunar dabi'ar ta kwankwadar miyagun kwayoyi.
Saurari rahotona sauti:
Dandalin Mu Tattauna