Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutanen Da ‘Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Dasu A Jihar Kebbi


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Yayin da wasu al'ummomi dake Arewacin Najeriya ke murnar nasarar da jami'an tsaro ke samu a kan ‘yan bindiga, wasu na nuna fargaba a kan bakin barayi da suke tuhuma na shiga yankunan su.

SKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da dakarun Sojin Najeriya suka fatattaki ‘yan bindiga tare da ceto mutanen da suke garkuwa da su fiye da 30 a jihar kebbi.

Yankin kudancin jihar Kebbi na daga cikin yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya da jama'a suke fuskantar cin zarafi daga ‘yan bindiga, kamar yankunan Bena, Wasagu, Fakai, Mahuta da dai sauransu.

To sai dai a karshen makon da ya gabata rahotanni sun nuna cewa dakarun Sojin Najeriya sun kai farmaki a sansanonin ‘yan bindiga dake yankunan kuma sun samu galaba a kan barayin.

Shugaban karamar hukumar Danko Wasagu, Hussaini Aliyu Bena wanda a farko ya sanar da cewa an ceto mutane 30 da aka yi garkuwa dasu, ya ce bayanan baya-bayan nan sun nuna adadin mutanen da dakarun suka ceto ya haura 30 abinda ya ta'allaka ga kwarin guiwa da gwamnati mai ci yanzu a jihar ke baiwa jami'an tsaro.

A dayan bangare kuwa a jihar Sakkwato dake makwabtaka da jihar Kebbin wasu jama'a ne ke nuna fargaba a kan wani samame da suka ga jami'an tsaro sun kai a wani wuri kuma suka kama mutanen da suke tuhumar munanan ‘yan ta'adda ne, inda muka samu zantawa da daya daga cikin masu fargabar.

Sai dai kakakin Rundunar 'yan sanda a jihar Sakkwato ASP Ahmad Rufa'I ya ce basu kai ga samun labarin ba.

Yankuna da dama ne a Najeriya ke fama da matsalolin rashin tsaro, inda mutane ke cike da bukatar samun magance matsalolin domin samun ci gaba.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

Sojojin Najeriya Sun Fatattakar ‘Yan Bindigan Da Suka Yi Garkuwa Da Mutum 30 A Jihar Kebbi.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG