SOKOTO, NIGERIA - Wasu mutanen da suka san mutumin sun yi ta nuna alhini yayin da wasu ke cewa abinda aka yi masa ya yi daidai.
Tun lokacin da bayani da hotunan kisan da aka yi wa Usman Buda suka bayyana a kafar sada zumunta a yanar gizo ta Facebook, bayanai ke ci gaba da yaduwa inda wasu jama'a musamman wadanda suka san shi kuma suna mu'amala da shi ke shakku akan abinda aka ce ya yi na batanci ga Annabi Muhammad SAW.
A hirar shi da Muryar Amurka, Yusuf Muhammad amini kuma makwabci ga marigayin ya ce, Usman mutumin kirki ne, mai son addini, kalaman batanci da aka ce ya yi ga Manzon Allah kage ne kawai aka yi masa.
Ya bayyana cewa, marigayin har Sallah yana jagorantar al'umma, da ace yana da matsala da ba'a bin sa a Sallah.
To sai dai a can mahotar Sakkwato inda abin ya faru jama'a sun tabbatar da cewa ya yi batanci ga Manzon Allah lamarin da ya kai ga kashe shi.
Rundunar 'yan sanda ta bakin kakinta a Sakkwato ASP Ahmad Rufa'i ta ce ta yi kokarin kubutar da shi, kuma ta karbe shi da ransa ta kai shi asibiti, sai dai daga baya rai ya yi halin sa amma dai tana kan gudanar da bincike.
Ita ma gwamnatin jihar Sakkwato ta fitar da wani bayani mai kira ga jama'a da su zauna lafiya.
A wani bayani mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamna Abubakar Bawa, an bayyana cewa, gwamnati zata duba lamarin, kuma ta yi wa jama'a kashedi daga daukar doka a hannunsu.
Yanzu dai dangin mamacin na cike da alhini da kuma juyayi akan abinda ya samu ‘dan uwan nasu, da ya riga mu gidan gaskiya.
Usman Buda ya kasance daya daga cikin jerin mutanen da aka kashe da sunan laifin batanci ga Annabi Muhammad SAW. Idan za a iya tunawa, irin haka ya faru a watan Mayu na 2022 a Kwalejin ilimi ta Shehu Shagari dake Sakkwato, da kuma wani makamancinsa da ya faru a babban birnin tarayya Abuja.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir: