Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’ummar Iyakokin Najeriya Da Nijar Na Fargaban Abun Da Zai Biyo Bayan Takunkumin ECOWAS


Taron ECOWAS
Taron ECOWAS

Yayin da yakin cacar baki ke dada zafafa tsakanin sojojin da suka karbe ragamar mulki a Nijar, da ECOWAS, AU da wasu kasashen duniya, wasu al'ummomi mazauna iyakokin kasar ta Nijar sun fara nuna fargaba a kan abin da kan iya zama illa gare su muddin ba'a warware tankiyar cikin ruwan sanyi ba.

Hakan ne ya sa masu sharhi a kan lamurran tsaro ke bayar da shawara a kan daukar matakai na tsirar da mazauna iyakokin kasar.

Tamkar yadda kasashe bakwai na Afirka suke da iyakoki da Jamhuriyar Nijar, haka Najeriya, tana da iyakoki da kasar a jihohi bakwai, da suka hada da Borno, Yobe, Jigawa, Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi.

Mazauna iyakokin sun bayyana cewa, duk abin da ya shafi Nijar suma ya shafe su saboda lura da yadda suke hulda da kasar cikin lumana da ‘yan uwantaka.

Tankiyar da ke tsakanin jagororin mulkin sojin kasar ta Nijar da Kungiyoyin Kasashen Afrika da ma wasu na duniya ta fara jefa fargaba cikin zukatan al'ummomi dake makwabtaka da Nijar kamar yadda wasu mazauna Kamba ta jihar Kebbi da Illela ta jihar Sakkwato ke nuna fargaba.

Dokta Yahuza Ahmad Getso, masani lamurran tsaro a Najeriya, ya ce duk da yake ba'a fatar kai wa ga amfani da karfin soji, amma kuma idan hakan ya kasance , ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi saurin daukar matakai na kubutar da al'ummomi dake zaune a iyakokinta da Jamhuriyar Nijar domin tsirar da su daga yaki.

Ya kara da cewa su kansu al'ummomi da ke zaune kan iyakokin, da zaran sun ga alamomi na amfani da karfin soji, su yi gaugawar kaucewa yankunan.

Yanzu dai takaddamar da ke tsakanin gwamnatin soji ta Jamhuriyar Nijar da kasashen Afirka da wasu kasashen duniya na ci gaba da daukar hankalin jama'a inda wasu su ke fatar ganin an samu bakin zaren warware ta cikin ruwan sanyi.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG