Idan za a iya tunawa, a ranar 17 ga watan Yuni na shekarar 2021 ne masu garkuwa da mutane suka afka makarantar sakandaren gwamnatin tarayya da ke birnin Yauri a jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya, suka sace dalibai da malamai, da wasu ma’aikatan makarantar.
Gwamnatin jihar Kebbi ta yi kokari wajen ceto wasu daga cikin daliban, amma da abin ya ci tura iyayen daliban da masu fafutaka sun ci gaba da kokarin ganin a sako sauran daliban.
Iyayen daliban sun kafa wani kwamiti wanda shi kuma ya bude wani asusu don neman taimako daga al’umma, gami da kaddarorin da iyayen suka sayar aka hada don ceto yaran.
Shugaban kwamitin Salem Kaoje, ya tabbatar wa Muryar Amurka da cewa lallai an sako yaran kuma za a mika su ga gwamnatin jihar Kebbi kafin a dankasu ga iyayensu.
Satar dalibai don neman kudin fansa dai ba sabon abu bane a Najeriya. Barayin daji sun taba kwashe yaran makaranta suka yi garkuwa da su a Kaduna, Neja da Katsina, lamaarin da ke ci gaba da barazana ga ilimi a yankin arewacin Najeriya.
Saurari karin bayani cikin sauti: