Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kara Himma Wajen Horas Da Jami'anta Kan Dabarun Tsaro


Taron rundunar sojoji
Taron rundunar sojoji

Yayin da rundunar sojin Najeriya ta himmantu wajen kimtsawa da karfafa gwiwar jami'anta domin su iya fuskantar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta, wasu mazauna yankunan da ke fama da rashin tsaro sun ce, sauki ya fara samuwa a yankunan su.

Wannan na zuwa ne lokacin da jami'an soji ke kara kutsa kai a yankunan da ke kokawa kan rashin tssro, domin magance ayukan 'yan bindiga.

Yanzu haka manyan kumandodin Sojin Najeriya na shiyar arewa maso yamma, da arewa maso gabas da na arewa ta tsakiya na kan halartar taron kara kimtsa su ga kyakkyawan shugabanci wanda ake yi sau hudu a shekara, wanda ke da manufar kara musu dubarun fuskantar kalubalen da Najeriya ke fuskanta a haujin tsaro.

Taron rundunar sojoji
Taron rundunar sojoji

Babban hafsan Mayakan kasa Manjo Janar Taoreed Lagbaja ta bakin Manjo Janar Kelvin Aligbe yace ana sa ran wannan taron ya karawa kumandodin basira ta yadda aikinsu zai kara samun nasara.

Yace alkiblar taron ita ce habaka basirar manyan kumandodin soji domin su iya fuskantar kalubalen tsaro a kowane muhalli, kuma wannan yana da cikin tsare-tsare na babban hafsan sojin Najeriya bisa bukatar sojin su kasance gogaggu, wadanda ke cikin shirin kota-kwana kuma masu kaifin basirar ganin rundunar sojin tana samun nasara ga aikin ta.

Rundunar sojoji
Rundunar sojoji

A daidai lokacin da Manyan kumandodin ke karbar horo, sauran dakarun soji sun bazama cikin dazuka na yankunan da ke fama da matsalolin rashin tsaro domin, magance matsalolin da samar da sauki ga al'ummomi.

Bello Isa Ambarura Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Illela da Gwadabawa, yankunan da suka sha fuskantar ayukkan ‘yan bindiga ya ce yanzu al'umma a yankunan suna bacci da idanu biyu rufe.

A cewar sa, a kowace safiya sojojin Najeriya na shiga dazukan da ke yankunan kananan hukumomi Gwadabawa da Illela suna farautar ‘yan bindiga, kuma sau da yawa ake ganin sun kamo mutanen da ake tuhumar barayin ne.

Har wa yau wasu mazauna yankunan da ke fama da matsalolin musamman na kananan hukumomin Gwadabawa da Illela sun tabbatar da cewa yanzu sauki yana samuwa, jama'a sun koma gonaki suna ayukkan noma gadan -gadan.

Babbar fatar jama'ar yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro, da ma dukan ‘yan Najeriya ita ce a sami saukin matsalolin rashin tsaro da suka dabaibaice kasar, ko da za'a sami sukunin fuskantar wasu matsaloli na daban, domin sai da zaman lafiya ake samun kowane ci gaba.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG