Wata takaddama ta kunno kai tsakanin Majalisar Dattawa da Babban Bankin Najeriya wato CBN, kan tsarin cire kudi a bankuna da CBN ya yi, abin da yawancin 'yan majalisar dattawan ke bada shawarar CBN ya soke, ko kuma ya kara yawan kudaden da za a cire a asusun bankuna, amma CBN ya ce ba za ta sabu ba.