Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Zikirullahi Kunle Hassan, ya ce cibiyar zata inganta aikin Hajji da Umrah da kuma bai wa kasar damar daidaita matsayin masana'antu a duniya.
Zikirullahi ya ce cibiyar za ta samar da hanyar koyon sana'o'i ga matasa da kuma zama wurin tuntuba a duk duniya, wajen koyar da aikin Hajji da Umrah.
Kwamishinan Bangaren Tsare-tsare na Hukumar Alhazan, Abdullahi Magaji Hardawa, ya ce yana cikin daliban farko da suka dauki darasi a cibiyar bayan an kaddamar da ita, ya yi bayani cewa ya shiga aji wajen daukan darasi da zumudi, domin ilimi shi ne sinadarin zaman duniya, saboda haka muddin ba ka da ilimi duniya za ta tafi ta barka a baya.
Hardawa ya ce ilimi na addini da ilimi na rayuwar yau da kullum abu ne da kowa ya kamata ya neme shi, saboda haka yana murna kwarai da wannan mataki da Hukumar ta dauka na kafa Cibiyar kuma yana ganin kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Shugaban Cibiyar, Farfesa Mohammed Nasirudin Maiturare, ya ce Cibiyar ita ce ta farko a Nahiyar Afirka kuma ba wuri ne da Ma'aikatan Hukumar Alhazai kadai za su yi koyo a ciki ba, har da dalibai daga fannoni daban daban na kasar.
Nasirudin ya ce za a samu takardar shaida na satifiket da difloma da digiri da kuma babban digiri.
Ma'aikatar ilimi ta Kasa ta amince da wannan Cibiya.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda: