Abuja, Nigeria —
Majalisar Dattawan Najeriya ta yi watsi da bukatar Shugaba Mohammadu Buhari ta amincewa da kashe wasu kudade wuri na gugar wuri har Naira triliyan 23.7 ba tare da an nemi izinin majalisar ba tun farko.
Wadannan Kudade ne da Babban Bankin Najeriya ya fito da su a shekaru 10 da suka wuce kuma ana kashe su babu izini. Majalisar ta dauki wannan matakin ne a bisa hujjar ba bi doka wajen neman amincewar ba.
Zauren Majilisar Dattawan ya rincabe inda sanatoci suka rinka gunaguni a daidai lokacin da Shugaban Kwamitin Kula da Harkokin Kudi, Solomon Adeola Olamilekan, ya gabatar da rahotonsa dake cewa Shugaba Mohammadu Buhari ya nemi Majalisar ta yi amanna da wasu kudade har Naira Triliyan 23.7 wadanda ya ce an riga an kashe su wajen yin hanyoyi da ayyukan cigaban kasar, tun shekaru 10 da suka wuce. Abin da ya dauki hankalin yan Majalisar shi ne cewa Babban Bankin Najeriya ne ya bada lamunin yin amfani da wadannan kudade ba tare da izinin majalisa ba.
Mohammed Ali Ndume yana cikin sanatocin da suka ki amincewa da yin amanna da wadannan kudade inda ya ce ba a kyauta wa Majalisar Kasa ba, domin in sun kawo wa Majalisa bukatun su, Majalisa tana ba bangaren Gwamnati hadin kai daidai gwargwado, saboda haka ba daidai ba ne a ce wa Majalisa ta yi amanna da kashe wadannan makudan kudade da suka isa kasafin kudin kasa na shekara, ba tare da an san yadda CBN ya bada su aka kuma kashe su ba.
A bisa doka dai, kamata yayi duk Kudin da za a kashe a kasar sai an kawo wa Majalisa ta amince tukuna sannan a kashe kudin, saboda haka zai yi wuya Majalisa ta yi amanna da wadanan kudade da aka riga aka kashe ba tare da sannin Majalisa ba, akan haka ne dan Majalisar Wakilai daga Jihar Gombe Yaya Bauchi ya ce akwai matsala a Majalisar. Yaya ya ce yana mamakin masu ilimin su da wadanda ke shugabantan su,ba sa amafani da hankali da tunani mai zurfi domin akwai cin hanci da rashawa a kasar. Yaya ya ce in ba a yi yaki da cin hanci ba kasa ba za ta mike ba.
Shi kuwa dan Majalisar Wakilai Mohammed Gudaji Kazaure ya ce Babban Bankin Najeriya ya bude kafa ta samu makudan kudade kuma ake dora masu haraji domin a yi sama da fadi da su. Gudaji ya ce dalilin da ya sa bankin ya matsa cewa kowa sai ya bude asusun ajiyar kudi a bankuna kenan.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya nada kwamiti a karkashin Shugaban Masu Rinjaye Ibrahim Abdullahi Gobir da zai yi aiki tare da Kwamitocin da ke kula da harkokin kudi da basukan cikin gida da na kasashen waje, har da Kwamitin Bankuna da Inshora da Kamfanonin hadahadar Kudi domin a gano musababbin fito da wadannan kudade daga Babban bankin kasa har a kashe su ba tare da amincewar majalisar kasa ba.
Majalisa ta tafi hutu zuwa ranan 17 ga watan Janairu na shekara 2023.
Saurari cikakken rahoton Madina Dauda: