Wannan ya kawo karshen jani-in-jaka da ya rika faruwa tsakanin Bashir Machina wanda aka aiyana cewa shi ne yi ci zaben fidda gwani a mazabar Yobe ta Arewan a maimakon Sanata Ahmed Lawan wanda ba a yi zaben fid da gwanin da shi ba tun farko.
A lokacin da aka zartar da hukuncin, uku daga cikin alkalai biyar da suka zauna akan shari'ar sun amince da matsayar APC cewa bai kamata a fara karar da aka shigar a gaban Kotun daukaka kara ta hanyar sammaci ba, tun da ta kunshi zarge zargen aikata zamba a kan wadanda suka daukaka kara.
Kotu ta ce a inda ake zargin zamba bai kamata a fara da sammaci na asali ba, saboda haka akwai bukatar a kira shaidu don tabbatar da zargin zamba. Abu na biyu kuma shi ne zargin Jamiyyar APC da zamba domin sauya sunan Machina da Lawan, a nan Kotu ta ce inda ake da zargin zamba akwai bukatar a kira shaidu don tabbatar da zargin zamba.
Alkalai uku sun amince da haka. Amma Alkalai 2, wato Adamu Jauro da Emmanuel Agim sun tabbatar da hukuncin Kotun daukaka kara.
To saidai ga masanin kundin tsarin mulki Barista Mainasara Kogo Umar ya yi nazari cewa wanan hukunci ya daure masa kai kwarai a matsayinsa na masanin shari'a, kuma shi ne ya sa ake cewa shari'a sabanin hankali.
Mainasara ya ce dokar zabe ta shekara 2022 karamin sashe na 29,30,31,32 da 33 sun ce wanda duk bai tsaya a zaben fid da gwani ba to ba za a sa sunan sa a wadanda za su tsaya takara ba.
Dokar ta kara jadadda cewa sai dai in dan takara yamutu shi ne za a iya sauya sunan sa.
Mainasara ya ce kashi na 115 na kundin tsarin mulkin kasa ya haramta mutum daya ya tsaye zabe a kujeru biyu lokaci daya. Saboda haka yana ganin ya kamata a jira a ji madogarar wanan hukunci daga wurin alkalan.
Shi ma kwararre a fanin siyasa da gudanar da mulki kuma malami a Jami'ar Abuja Forfesa Abu Hamisu ya yi tsokaci cewa an yi wa Dimokradiya karan tsaye. Hamisu ya ce abinda ya faru a Kotun Koli ba dimokradiya ba ne, kuma ba a bi kundin tsarin mulki ba ko kadan, domin Ahmed Lawan bai ma tsaya takarar kujerar sanata ba sai na kujeran shugaban kasa.
Hamisu ya ce wasu 'yan kalilan ne ke rike da kasar a hannun su, suke juya ta yadda suke so. Hamisu ya ce abinda ya dauki hanakali shi ne sun manta cewa talakawa ne ke zabe ba Kotu ba, kuma talakawa sun gani sun kuma shaida abinda ya faru, zabi ya rage gare su.
Amma Sanata Ahmed Lawan ya yaba da hukuncin inda ya ce wannan ya nuna cewa dimokradiya ce ta taka rawa mai muhimmanci a wannan lamarin. Sabodaa haka yana murna.
Na yi kokarin samun mai magana da yawun Bashir Machina domin in ji ra'ayinsu a game da hukuncin amma bai amsa waya ta ba.
Saurari rahoton: