Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ta Yi Kira Ga Hukumomin EFCC Da ICPC Da Su Kama Dan Takarar PDP Atiku Abubakar


Festus Kyamo
Festus Kyamo

Jamiyyar APC mai mulki ta yi kira ga hukumar EFCC da ICPC da su kama dan takaran kujeran shugaban kasa na jamiyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar akan zargin da aka yi cewa an hada baki da shi an yi sama da fadi da dukiyar al'umman Najeriya.

Amma PDP sun ce APC tana fama da "PANTAPHOBIA", wato matsalar tsoro a turanci.

An ce "kallo ya koma sama da shaho ya dau giwa". Jamiyyar APC mai mulki a Najeriya ta bukaci hukumar yaki da masu yi wa kasa zagon kasa ta EFCC da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da laifuka masu alaka da haka ICPC da hukumar da'ar ma'aikata wato CCB, da su hanzarta kamo dan takarar shugaban kasa na jamiyyar PDP, Atiku Abubakar bisa zargin cin hanci da rashawa.

kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jamiyyar
kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jamiyyar

A lokacin da yake wa manema labarai jawabi, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jamiyyar APC Festus Keyamo ya nuna wata takarda mai dauke da kwanan wata 16 ga Janairu na shekara 2023 da ya riga ya shigar da kara a kotu, yana neman hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su kamo Atiku Abubakar a bisa laifuka da suka shafi halatta kudaden haram, karya dokar da'a, hada baki da kuma aikata cin amana da almubazaranci.

kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jamiyyar
kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jamiyyar

Daya cikin 'ya'yan kwamiti yakin neman zaben shugaban kasa na jamiyyar APC Mohammed Idris Malagi ya yi karin haske yana cewa wanan bukata da APC ta baiyana ya biyo bayan zargin da wani matashi, Micheal Achimugu ya yi ne, inda ya ce shi tsohon mataimakin dan takarar jamiyyar PDP ne tun lokacin da ya ke mataimakin shugaban kasa.

kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jamiyyar
kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jamiyyar

Malagi ya ce wasu rubuce rubuce da kuma faifan bidiyo da Achimugu ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya zargi Atiku da yin amfani da wasu motoci na musamman, masu suna SPV da aka sayo wajen yin damfarar makudan kudade.

Malagi ya ce Achimugu ya bayar da kwararan hujjoji da suka sa shi zargin Atiku Abubakar da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo. Malagi ya ce an yi makonni biyu da yayata zargin da Achimugu ya yi a shafukan sada zumunta kuma babu mutum daya da ya fito ya karyata shi, shi ya sa Jamiyyar APC ta ke kira da a yi bincike mai zurfi domin a ba 'yan kasa hakkin su na sanin gaskiyar al'amarin.

A lokacin da ya ke mayar da martani a game da matakin da APC ta dauka akan dan takara shugaban kasa a jamiyyar PDP Atiku Abubakar, mai magana da yawun kwamitin neman zaben shugaban kasa na jamiyyar, Daniel Hassan Bwala ya ce dan takarar shugaban kasa a jamiyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya na fama da matsanancin tsoro wanda aka sani da Pantaphobia.

Bwala ya ce, jamiyyar APC tana ba shi kunya, domin ba ta damu da wahala da radadin talauci da 'yan Najeriya ke fama da shi ba, sai wasu maganganu mara tushe. Bwala ya ce Atiku Abubakar yana cikin manyan 'yan kasa da hukumar EFCC ta yi binciken kwaf kwaf akansa fiye da kowa.

Bwala ya ce su ba su san Micheal Achimugu ba, kuma ba su ga dalilin da zai sa su yi cacar baki da shi a shafukan sada zumunta ba. Bwala ya ce dan takarar shugaban kasa na Jamiyyar APC ya san ba zai ci zabe ba shi yasa yake amfani da sojojin haya irin su Achimugu saboda su bata wa Atiku suna. Amma Allah Ya fi su.

Jamiyyar APC ta bukaci Atiku Abubakar ya janye daga takarar kujerar shugaban kasa domin ya saba wa sashe na 5,10,13,da 17 na dokar da'ar ma'aikata.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00
XS
SM
MD
LG