Kwamitin wucin gadi da majalisar wakilai ta nada kan sabbin tsare-tsare na Naira da manufar musayar Naira, ya yi watsi da karin wa'adin kwanaki 10 da babban bankin Najeriya na CBN ya yi don musayar tsofaffin takardun kudi.
Shugaban kwamitin kuma shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana wa Muryar Amurka cewa doka ta 20 karamin sashi na 3.4, 4, da 5 na dokar da ta kafa babban bankin kasar ba ta ba da hurumin daukar wannan mataki ba.
Doguwa ya ce gwamnan bankin Najeriya da bankin na CBN kansa, ba su ne suka yi kansu ba, doka ce ta kasa ta yi su kuma ita ta basu dama su yi abin da ake kira canza kudi daga yanayin da su ke zuwa sabon tsari ko sabon salo, wannan dokar ta ce babu wani sashinta da ya haramta amfani da tsofaffin kudi a lokacin da aka canza su har sai lokacin da suka kare a kasuwanni ko a hada-hadar cinikayya.
A nasa hangen, me zai sa gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ki amsa kiraye-kirayen da 'yan majalisar kasa suka yi masa, da kuma 'yan kasa da ke Kudu da Arewa, Gabas da yamma?
Ya kara da cewa, yana ganin akwai siyasa a cikin al'amarin domin Emefiele ya taba neman tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC, daga baya sanin cewa doka ba ta ba shi dama ya zama dan siyasa ba, sai ya sauka. Wannan mataki ya janyo cece-ku-ce har wasu ma na ganin ya kamata ya sauka daga mukamin nasa.
Abin da majalisa ke bukata shi ne a bi doka kawai ba karin kwanaki 10 ko kwana 14 ba, a cewar Doguwa.
To ko wane mataki majalisa za ta dauka akan Emefiele idan ya kekasa kasa ya ce ba zai kara wa'adin fiye da kwanaki 10 ba?
Doguwa ya ce har yanzu majalisa tana jiransa ya gurfana a gabanta, kuma bai fi karfin doka ba. Bayan haka majalisa za ta nemi sufeto Janar na 'yan sanda ya kawo masu Emefiele, ko kuma majalisa ta shigar da kara kotu domin a yi canjin kudin ta hanyar da ba za a takura wa al'umma ba, ba zai shafi harkar zaben kasa da ke karatowa ba, kuma ba zai shafi mulkin jam'iyyar APC ba, domin ga dukkan alama Emefiele bai tanadar wa kasa alheri ba kuma majalisa ba za ta yarda da wannan ba.
A ranar Lahadi ne gwamnan babban bankin ya kara wa'adin canjin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu na wannan shekara, bayan da ya je Daura inda ya gana da Shugaba Mohammadu Buhari.
Saurari hirar Medina Dauda cikin sauti: