Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arzikin Arewacin Najeriya Zai Inganta Bayan Gano Man Fetur A Jihar Nasarawa - Masana


Sa'o'i kadan bayan da kamfanin NNPC ya bada sanarwar samun Man fetur a Jihar Nasarawa da ke Arewa ta tsakiya a Najeriya, masu ruwa da tsaki sun bada ra'ayoyi mabanbanta a game da al'amarin.

ABUJA, NIGERIA - Wasu na murna amma wasu na korafin cewa rashin shugabanci na gari na iya shafan wannan baiwa da Allah ya yi wa Arewa a wannan lokaci.

Hedikwatar NNPC
Hedikwatar NNPC

Wata takarda mai dauke da sa hannun babban jami'in hulda da manema labarai na kamfanin NNPC Garbadeen Mohammed, ya bayyana cewa shugaban kamfanin Man Fetur na kasar Mele Kolo Kyari ya ce karshen kwatan farko na wannan shekara ne, watan Maris kenan, za a fara aikin hakkar man fetur a Keana ta Jihar Nasarawa.

Garbadeen ya ce ayyukan bincike sun gano cewa akwai man fetur mai yawa a Jihar ta Nasarawa, kuma kamfanin a shirye ya ke ya yi aikin da ya dace don samo man gami da albarkatun iskar gas a cikinsa.

Wannan mataki ya gamsar da mataimakin shugaban kungiyar dillalan Man Fetur ta kasar wato IPMAN, Abubakar Maigandi Dakingari inda ya bayyana ra'ayinsa cewa wannan labari ne mai dadi sosai kuma da shi da ‘yan kungiyar IPMAN sun yi farin ciki kwarai da gaske, saboda wannan samun mai da aka yi a Nasarawa da sauran wurare a Arewa abu ne mai muhimmanci, kuma abu ne wanda zai inganta arzikin Arewacin Najeriya.

Abubakar Salihu Butu Shugaban IPMAN Adamawa
Abubakar Salihu Butu Shugaban IPMAN Adamawa

Maigandi ya ce ba ma a Arewaci ka dai ba, duk kasar Najeriya za ta samu wadata kuma zai kawo kulla zumunci mai karfi tsakanin Arewaci da Kudancin kasar.

Maigandi ya ce dama a Kudancin kasar ne kadai ake da man fetur amma yanzu gashi an samu a Arewa a wurare da dama, saboda haka kungiyar su a shirye ta ke a dama da ita wajen kawo wa ‘yan kasa ribar samun man.

Amma ga babbar 'yar siyasa kuma mai gwagwarmayar ganin an kawo wa Arewa ci gaba Naja'atu Mohammed ta yi korafi da nuna damuwa akan abinda ta kira rashin shugabanci nagari.

Naja ta ce idan za a yi la'akari da yadda samun arzikin man fetur ya kawo wa Kudancin kasar matsala da rikice-rikice iri daban-daban, za ta yi zullumin samun man fetur a Arewa.

Naja’atu Muhammad
Naja’atu Muhammad

Naja ta ce rashin shugabanci na gari na iya jefa Arewa a cikin halin ha'ula'i domin za a tada mutane daga muhallan su kuma ba za a yi masu komi ba.

Naja ta kara da cewa dama manyan kasa ne ke hada baki da ‘yan wasu kasashe suna sace man kasar, tare da raba kudaden da ake samu a tsakanin su. Ta ce sai an hada da rokon Allah domin a samu shugabani masu kishin kasa a zabe mai zuwa in ba haka ba tana ganin zai zama abin takaichi.

Shi kuwa masanin harkokin tattalin arziki na kasa da kasa, Shuaibu Idris Mikati, ya ce abin alfahari ne samun mai a shiyar Arewa, kuma yanzu an samu ci gaba a kimiya da fasaha da ba za a samu matsalar pasa bututan mai kamar yadda ake yi a shiyar Neja Delta ba.

Mikati ya ce a kasashe irin su Saudi Arabiya, ba a jin matsaloli a fannin man fetur ko kadan. Mikati ya ce ma'adinan Arewa suna da kyau da muhimmanci wajen kera abubuwa daban-daban irin su batur na mota da na wayar hannu, da abubuwan ci gaba da dama.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne shugaban kasar Mohammadu Buhari ya kaddamar da aikin hakko danyen mai na farko a Arewacin Najeriya a Kolmani da ke kan iyakar Jihohin Bauchi da Gombe.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Masu Ruwa Da Tsakin Najeriya Sun Fara Ce-ce-ku-ce Game Da Samun Man Fetur A Jihar Nasarawa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

XS
SM
MD
LG