A Najeriya, takkaddama ce ta kunno kai tsakanin Gwmanati da Kungiyoyin Kwadago akan batun karin albashi da ya kamata a fara tun watanni uku da suka gabata, amma har yanzu ana ci gaba da gwagwarmaya da ya hana a cimma matsaya, balle har a tsayar da yawan kudaden da za a kara wa ma'aikatan.