Daya daga cikin su Komred Mohammed Abubakar Gombi wanda ya taho daga Jihar Adamawa ya baiyana wa wakiliyar Muryar Amurka cewa, tunda shugaban kasa ya sa hannu a dokar da ta bada damar a basu aiyukan yi, babu wanda ya dube su, duk da cewa sun sha zuwa wurin wannan hukumar domin neman hakkinsu.
Abubakar ya ce suna neman kashi 5 cikin 100, na mukamai da zu su rarraba a tsakanin miliyoyin 'yan uwansu da ke Najeriya.
Shi ma mai magana da yawun kungiyar masu Larurar Gani ta kasa, Komred Muktari Saleh ya ce suna rokon shugaba Mohammadu Buhari, da ya taimaka ya bi takwararsa na Ghana, ya basu mukamin Minista, domin a cewar sa suna da masu digiri na farko, da na biyu, da na uku, da ma wadanda suke Farfesa a cikinsu.
Ya kuma ce ai hankali da ilimi ne ke aikin Minista ba batun gani ko yin amfani da hannu, ko kafafu ba. Muktari ya ce za su ma iya rike amana fiye da wasu masu ganin.
Jami'ar hulda da manema labarai ta hukumar daukan ma'aikata ta kasa Felicia Eniola, ta ce hukumar na daukan matakan sharewa Masu Larura ta Musamman hawaye, amma a halin da ake ciki yanzu shugaban hukumar, da babban sakataren hukumar suna halartar wani muhimmin taro a fadar shugaban kasa.
To sai dai mai fashin baki a al'amuran yau da kulum, kuma masanin kundin tsarin mulki, ya ce dokar kasa ta tanadi fannoni daban daban da ya ba Masu Larura ta Musamman dama, na a yi masu adalci, sannan a bari su yi walwala a duk inda suke so, saboda haka hakki ya rataya a wuyan mahukunta.
Ga cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.
Facebook Forum