Gwamnatin Jihar Zamfara ta cimma wata yarjejeniya ta kudi dallar Amurka Biliyan daya, wato kimanin naira biliyan dari uku da sittin, da Bankin raya Kasashen Afrika da ke kasar Masar.
Gwamnan Jihar Alhaji Bello Matawallen Muradun, shi ne ya sa hannu a wannan yarjejeniya a babban birnin tarayya Abuja.
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawallen Muradun, ya ce, wadannan kudade za a yi amfani da su ne wajen gina jihar Zamfara, domin farfado da tattalin arzikin jihar, ta gina sabon filin sufurin jiragen sama, da na jirgin kasa, farfado da masana'antu, gina asibitoci, gina kwata ta zamani, samar da ruwan sha, kana da samar da wutan lantarki.
Gwamna Matawalle, ya ce, babu tsayyayen wa'adi na yin aiki da wadan nan kudade, tunda ba bashi aka karbowa jiha ba, bankin ne zai zo da kwararru wajen zuba jari a wadanan bangarorin da jihar ke bukata.
Da yake amsa tambaya akan tsugunar da wadanda iftila'i ya sa suka bar matsugunan su, gwamnan ya ce, shugaba Mohammadu Buhari ya ba da tallafi na kayan abinci da taki, saboda mutanen su yi noma, gwamnatin jiha ta ce za ta bada filin noma ga duk dan jihar mai so yayi noma.
A batun nasara da ya samu cikin watanni kalilan da kama aiki, gwamnan ya ce, ya nemi hadin kan dukanin ‘yan jihar daga jam’iyyu daban-daban domin ci gaban jihar.
Facebook Forum