Femi Gbajabiamila dake zaman kakakin Majalisar Wakilai na Najeriya, ya sanar da shugabanin Kwamitoci 106 sannan ya ‘kara da wasu guda uku na rikon kwarya wanda ya kawo jimlar kwamitoci 109.
A cikin sabbin kwamitocin akwai kwamitin kula da asusun jama'a wanda ‘dan Majalisa Woleoke zai shugabanta.
A tsofaffin kuma, kwamitin kula da kasafin kudi ya koma hannun Muktar Aliyu Betara. Shi kuma Jimi Benson zai jagoranci kwamitin kula da bangaren tsaro. Paschal Obi kuma zai duba kwamitin kula da cibiyoyin lafiya na kasa.
Sai kuma kwamitin yaki da cin hanci da rashawa wana aka nada Nicholas Shehu domin ya jagoranta. Abdulrazak Namdas wanda ya kula da kwamitin hulda da manema labarai a Majalisar ta 8, yanzu zai kula da kwamitin rundunar soji.
Bayan da aka kammala raba kwamitocin an samu labarin korafe-korafe da wasu suka yi, amma Dakta Abdullahi Balarabe Salame ya ce duk adalcin da za a yi, in dai maganar rabo ce to sai an samu masu korafi, haka kuma ya tabbatar da cewa kakakin Majalisar ya yi rabon ga dukkan shiyoyin nan shida na ‘kasa.
A nashi nazarin Kabir Ibrahim Tukura, ya ce ‘kara yawan kwamitocin ba zai ‘kara yawan kudaden gudanarwa ba, amma zai kawo saukin aikin sa ido da Majalisa ke yi kan yadda ake kasafta kudaden gwamnati, wanda yin hakan zai kara nasara ga yaki da cin hanci da rashawa, ya kuma sa ayi ayyukan da zasu kawo wa al’umma jin dadin rayuwa.
Domin Karin bayani saurari rahotan Medina Dauda daga Abuja Najeriya.
Facebook Forum